Lauyan Yara da Su Ka Yi Zanga Zanga Ya Fadi Yadda Gwamna Abba Ya Agaza Masu
- Barista Hamza Nuhu Dantani ya ce gwamna Abba Kabir Yusuf ya jajirce a wajen ceto yaran Kano da aka garkame
- Lauyan ya yabi gwamnatin Kano kan yadda gwamna da kansa ya kira shi a kan matsalar yaran da aka tsare
- Ya shawarci jagororin Arewa da su yi koyi da dattakon Abba Kabir Yusuf da tausayin mutanen da ya ke mulka
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano - Lauyan yaran nan 73 da gwamnatin Tinubu ta cafke daga Kano bisa zargin yunkurin kifar da ita, Barista Hamza Nuhu Dantani ya bayyana yadda gwamnan Kano ya kawo masu agaji.
Barista Hamza Nuhu Dantani ya ce kafin gwamna Abba Kabir Yusuf ya tuntube shi, ya yi kokarin tuntubar wasu manya a kasar nan, amma aka yi biris da shi.
A wani bidiyo da Ibrahim Adam ya wallafa a shafinsa na Facebook, Barista Hamza Nuhu Dantani ya ce daga cikin wadanda ya tuntuba akwai Ordinary President na shirin Brekete da wasu manya a Kano.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
"Samun mutum kamar Abba da wuya"- Lauya
Barista Hamza Nuhu Dantani ya bayyana cewa da kansa gwamna Abba Kabir Yusuf ya tuntube shi a kan batun yaran da gwamnatin tarayya ta gurfanar a gaban kotu.
Ya zazzaga ruwan yabo ga halayyar Abba Kabir Yusuf na kaskantar da kai da jagoranci da adalci, wanda ya taimaka wajen kubuto da yaran.
"Abba bai san an kulle yara ba:" Barista
Lauyan yaran da gwamnati ta janye tuhumar cin amanar kasa da ta ke yi masu, Barista Hamza Nuhu Dantani ya ce gwamna Abba Kabir Yusuf ya shaida masa cewa bai san yara kanana aka kama ba.
A cewarsa, hukumomi sun sanar da gwamna cewa an kama wasu mutane da ke kokarin juyin mulki a kasar nan, kuma wannan babban lamari ne da ke bukatar bincike.
Gwamna Abba ya gana da yara
A baya kun ji cewa gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya tattauna da yaran da gwamnatin tarayya ta saki bayan janye tuhumar cin amanar kasa da kokarin juyin mulki kan zababbiyar gwamnati
Gwamnan Abba Kabir Yusuf ya ja kunnen yaran da su tabbata sun mayar da hankali a kan karatunsu da kokarin zama mutane na gari domin cimma bukatunsu a nan gaba.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng