Ana Jimamin Mutuwar Janar Lagbaja, Tsohon Hafsan Tsaro Ya Yi Babban Rashi
- Matar tsohon hafsan tsaron Najeriya, Admiral Ola Sa'ad Ibrahim ta rasu bayan fama da gajeruwar jinya a birnin Abuja
- Marigayiyar mai suna Aminat Dupe Ibrahim ta rasa ranta a Abuja a daren jiya Talata 5 ga watan Nuwambar 2024
- Wannan na zuwa ne yayin da ake jimamin rasuwar hafsan sojoji, Laftanar-janar Taoreed Lagbaja wanda ya rasu a Lagos
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
FCT, Abuja - Tsohon hafsan tsaron Najeriya, Admiral Ola Sa'ad Ibrahim ya gamu da babban rashi na matarsa.
Marigayiyar mai suna Aminat Dupe Ibrahim ta rasu ne a daren jiya Talata 5 ga watan Nuwambar 2024 a Abuja.
Yauhe matar tsohon hafsan tsaro ta rasu?
Vanguard ta tabbatar da cewa marigayiyar ta rasu ne a Abuja bayan fama da gajeruwar jinya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Rahotanni sun tabbatar da cewa Aminat ta rasu ta bar mijinta, Ola Ibrahim da kuma 'ya'ya da tulin jikoki.
Mijin marigayiyar ya rike mukamin hafsan tsaron Najeriya daga shekarar 2012 zuwa 2014 a mulkin Goodluck Jonathan.
Kafin zama hafsan tsaron Najeriya, ya rike mukamin hafsan sojojin ruwa a kasar daga 2010 zuwa shekarar 2012.
An sanar da lokacin sallar jana'izar matar hafsu
Wata majiya ta tabbatar da cewa za a yi sallar jana'izar marigayiyar a yau Laraba 6 ga watan Nuwambar 2024, cewar Punch.
Za a gabatar da sallar a babban masallacin Abuja a yau da misalin karfe 1:30 bayan sallar Azahar.
Sannan an tabbatar da cewa za a raka gawar marigayiyar zuwa makabartar Musulmai ta Gudu da ke Apo da ke birnin Abuja.
Hafsan sojoji, Laftanar-janar Lagbaja ya rasu
Kun ji cewa an shiga jimami a Najeriya yayin da aka samu labarin rasuwar Janar Taoreed Abiodun Lagbaja, babban hafsan sojin kasa.
Fadar shugaban kasa, ta hannun Bayo Onanuga, mai magana da yawun Bola Tinubu ta sanar da rasuwar a ranar Laraba 6 ga watan Nuwambar 2024.
Sanarwar ta ce babban hafsan sojin kasan, Lagbaja ya rasu ne a daren ranar Talata 5 ga watan Nuwambar 2024 a Legas bayan fama da rashin lafiya.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labari
Asali: Legit.ng