Bayan Sun Shaki Iskar Yanci, Gwamnan Kano Ya Ja Kunnen Yara kan Zanga Zanga

Bayan Sun Shaki Iskar Yanci, Gwamnan Kano Ya Ja Kunnen Yara kan Zanga Zanga

  • Gwamna Abba Kabir Yusuf ya gargadi yaran da ta karbo daga hannun gwamnatin tarayya da kar su kara shiga zanga zanga
  • Gwamnatin Kano ta ce babu abin da ya dace yaran su rika yi a yanzu kamar zuwa makaranta da kuma zama yan kasa na gari
  • A yammacin Talata yaran Kano akalla 73 su ka sauka a jihar bayan shafe tsawon lokaci a hannun jami'an tsaron kasar nan

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano Gwamna Abba Kabir Yusuf ya ja kunnen kananan yara a kan batun zanga zanga da za a iya gudanarwa a nan gaba.

Kara karanta wannan

Gwamna Abba ya aika sako ga Tinubu bayan ya karbi yaran da aka tsare

Gwamnan ya yi gargadin a lokacin da ya ke ganawa da yaran a asibitin kwararru na Muhammadu Buhari inda ake duba lafiyarsu.

Gwamnati
Abba ya shawarci yaran da gwamnati daina shari'a da su Hoto: Abba Kabir Yusuf
Asali: Facebook

Jaridar Vanguard ta wallafa cewa bayan ganawar yaran da gwamnan Kano, an raka su bangaren da za a kula da kowannensu a asibitin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamna Abba ya ja kunnen yaran Kano

Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf ya hori yaran da gwamnatin tarayya ta daina shari’a da su da kar su kara shiga wata zanga zanga a nan gaba.

Ya shawarce su da su duba irin wahalar da su ka shiga saboda zanga zanga, inda ya nemi su zama yan kasa na gari a duk inda su ke.

Gwamna ya shawarci yara su dauki darasi

Gwamnatin jihar Kano ta shawarci yaran da su ka shaki iskar yanci bayan shafe tsawon lokaci a tsare da su shiga taitayinsu.

Kara karanta wannan

Zanga zanga: Kashim Shettima zai tarbi yara bayan gwamnati ta janye shari'a a kotu

Ya shawarce su da su zamo yan kasa na gari ta hanyar neman ilimi da amfani da shi wajen cimma burinsu a nan gaba.

Gwamnan Kano, Abba ya godewa Tinubu

A baya mun ruwaito cewa gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf ya mika godiyarsa ga shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu da ya bayar da umarnin daina shari’a da wasu kananan yara.

Jami’an tsaron kasar nan sun cafke kananan yaran a jihohi daban-daban a lokacin da jama'a su ka fito zanga zanga domin nuna adawa da yunwa da tsare-tsaren gwamnatin Tinubu.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labari

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.