Kwana Ya Kare: Mutane Sama da 15 Sun Mutu a Kan Gadar Sama, Bayanai Sun Fito

Kwana Ya Kare: Mutane Sama da 15 Sun Mutu a Kan Gadar Sama, Bayanai Sun Fito

  • Hatsarin mota ya laƙume rayukan mutum 16 a kan gadar Njaba da ke karamar hukumar Njaba a jihar Imo ranar Talata
  • Ganau da lamarin ya faru a kan idonsu sun ce motar hayan ta kuccewa diraban, ta bugi gefen gadar sannan ta faɗa cikin kogi
  • Rahotanni sun nuna suka fasinjojin da ke ciki sun mutu nan take yayin da ake dakon sanarwar yan sanda a hukumance

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Imo - A kalla mutane 16 ne suka rasa rayukansu a wani hatsarin mota da ya afku a kan gadar Njaba da ke karamar hukumar Njaba ta jihar Imo.

Mummunan hatsarin ya afku ne yau Talata, 5 ga watan Nuwamba, 2025 a gadar da ke kan babban titin Owerri-Orlu a Kudu maso Gabashin Najeriya.

Kara karanta wannan

Bayan masifar yan bindiga, wasu gungun miyagu daban sun sake bulla a Sokoto

Hope Uzodinma
Mummunan hatsarin mota ya hallaka mutum 16 a wata gadar sama a Imo Hoto: Hope Uzodinma
Asali: Twitter

Jaridar Leadership ta ruwaito cewa ana yawan samun afkuwar haɗurra a gadar Njaba tare da asarar rayuka da dama.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda mutum 16 suka rasu a Njaba

Wani ganau da hatsarin ya afku a kan idonsa ya ce motar hayan ta ci ƙarfin direban, inda ta zarce ta faɗa ruwan da ke gefen gadar.

Ya bayyana cewa sai ta motar ta tunkuyi bakin gabar titin kafin daga bisani ta fada cikin kogin.

Sakamakon matsatsi da cunkoson da aka yi a cikin motar da munin hatsarin da ma cewa ya zo da karar kwana, ko mutum ɗaya daga cikin fasinjojin bai tsira ba.

Mutane sun kai ɗauki bayan hatsarin

Bayanai sun nuna cewa lokacin da mutanen yankin suka yi gaggawar faɗawa kogin domin ceto fasinjojin, sun taras da duka Allah ya masu rasuwa.

Har kawo yanzu, jami'in hulɗa da jama'a na rundunar ƴan sandan jihar Imo, Henry Okoye, bai fitar da wata sanarwa a hukumance kan faruwar lamarin ba.

Kara karanta wannan

JAMB: Dubun 'Farfesa' ya cika, an garkame shi kan yunkurin rubutawa yarsa jarabawa

Amma rahotanni sun nuna cewa mutanen da ba su ga ƴan uwansu sun yi cincirindo a wurin domin duba ko suna cikin waɗanda hatsarin ya rutsa da su.

Bom ya tashi a kasuwar Orlu

A wani labarin, rahotanni sun nuna cewa wani bom da miyagu suka dasa ya tarwatse a kasuwar Orlu da ke jihar Imo a Kudu maso Yamma

Jami'in hulɗa da jama'an na rundunar ƴan sandan jihar, Henry Okoye ya ce bom din ya tashi da masu ƙokarin dasa shi kuma sun mutu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262