Yaran Zanga Zanga Sun Kara Samun Gata, An Dauki Nauyin Karatunsu
- A yau ne alkalin kotun tarayya ya tabbatar da bukatar gwamnatin Ahmed Tinubu na wanke yaran zanga zanga daga laifi
- Biyo bayan lamarin, ƙungiyar makarantu masu zaman kansu ta Najeriya ta yi alkawarin ɗaukar nauyin karatun yaran
- Kungiyar ta ce ba wannan ne karon farko da ta ke ayyukan jin kai ba, ta ce dama ta saba tallafawa marasa karfi a Najeriya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Lagos - Ƙungiyar makarantu masu zaman kansu ta kasa (NAPPS) ta yi alkawarin ɗaukar nauyin karatun yaran zanga zanga.
An ruwaito cewa kungiyar NAPPS ta bayyana haka ne yayin wani taro da ta yi a jihar Legas.
Jaridar Vanguard ta wallafa cewa shugaban kwamitin amintattun NAPPS, Abdulmumini Kundak ne ya tabbatar da lamarin.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An dauki nauyin karatun yaran da aka kama zanga zanga
Kungiyar makarantu masu zaman kansu ta fitar da shirin tallafawa yaran zanga zanga da aka kama.
Shugaban kungiyar, Abdulmumini Kundak ne ya yi alkawarin jim kadan bayan gwamnatin tarayya ta yi musu afuwa.
Matakin karatun yaran da NAPPS za ta dauka
Kungiyar NAPPS ta bayyana cewa za ta dauki nauyin karatun ne a matakin makarantun firamare da sakandare.
NAPPS ta ce za a zakulo waɗanda shekarunsu bai wuce shiga firamare da sakandare ba sai ta dauki nauyin karatunsu.
A ina yaran za su yi karatu?
Kungiyar NAPPS ta bayyana cewa wadanda aka dauka za su yi karatun ne a jihohin da suke ba tare da canza musu gari ba.
A cewar kungiyar, tana da tsarin da ta ke bi wajen tallafawa masu rauni a dukkan sassan Najeriya.
Kungiyar ta ce akwai buƙatar a ba yaran kulawa domin su zamo yan kasa na gari da za su kawo canji a Najeriya.
Zanga zanga: Za a binciki yan sanda
A wani rahoton, kun ji cewa rundunar yan sandan Najeriya ta ce za ta binciki jami'an da ake zargi da azabtar da yaran zanga zanga.
Sufeton yan sanda, IGP Kayode Egbetokun ne ya tabbatar da haka bayan shugaba Bola Tinubu ya sanar da yin afuwa ga yaran.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng