Gwamna Abba Ya Aika Sako ga Tinubu bayan Ya Karbi Yaran da Aka Tsare
- Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya yaba da matakin da shugaban ƙasa ya ɗauka na sakin yaran da aka tsare saboda zanga-zanga
- Abba ya nuna godiyarsa ga shugaba Bola Tinubu kan yadda ya sake ba yaran dama duk da girman laifin da ake tuhumarsu da aikatawa
- Ya bayyana cewa za a mayar da yaran cikin al'umma ta hanyar sanya su cikin makaranta ta yadda za su amfani kansu da jama'a baki ɗaya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Kano - Gwamnan jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya yi magana kan yaran da aka sako waɗanda aka tsare saboda zanga-zanga.
Gwamna Abba Kabir ya nuna godiyarsa ga shugaban ƙasa Bola Tinubu kan yadda ya saurari kiraye-kirayen da jama'a suka yi na a saki yaran 76 da ake tsare kan zanga-zangar.
Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun bakin gwamnan, Sanusi Bature Dawakin Tofa, ya sanya a shafinsa na Facebook.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamna Abba ya yi godiyar ne bayan ya karɓi yaran daga wajen mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima, a fadar Aso Rock.
Me Gwamna Abba ya ce kan Tinubu?
Gwamnan ya nuna godiyarsa ga shugaba Tinubu saboda fahimtar da ya nuna da sake ba yaran dama.
Yaran guda 76 waɗanda aka tsare saboda zanga-zangar, za a dawo da su Kano, inda za a duba lafiyarsu kafin a sada su da iyalansu.
Gwamna Abba ya ba da tabbacin cewa za a mayar da yaran cikin al'umma ta hanyar sanya su a makaranta da ba su damar sake gina rayuwarsu.
"Duk da girman tuhume-tuhumen da ake yi musu, mun fahimci muhimmancin sake ba waɗannan yaran dama."
"Duk da abin da suka yi abin nadama ne, matsayinsu na ƙananan yara bai kamata ya hana su samun damar gyaruwa domin da ta su gudunmawar a cikin al'umma ba."
- Gwamna Abba Kabir Yusuf
Shettima ya faɗi dalilin sakin yaran da aka tsare
A wani labarin kuma, kun ji cewa mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima ya ce Bola Tinubu ya ba da umarnin sakin kananan yaran da aka kama saboda tausayi.
Shettima ya bayyana haka ne a lokacin da ya karbi bakuncin yaran a fadar shugaban ƙasa ranar Talata, 5 ga watan Oktoba, 2024.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng