Kashim Shettima Ya Fadi Asarar da Aka Tafka saboda Zanga Zanga

Kashim Shettima Ya Fadi Asarar da Aka Tafka saboda Zanga Zanga

  • Mataimakin shugaban ƙasa ya koka kan asarar da aka tafka sakamakon zanga-zangar #EndBadGovernance a watan Agustan 2024
  • Kashim Shettima ya bayyana cewa an yi asarar sama da N300bn sakamakon zanga-zangar wacce aka gudanar a faɗin ƙasar nan
  • Shettima ya bayyana hakan ne lokacin da ya karɓi yaran da aka tsare saboda zanga-zangar bayan Bola Tinubu ya yi musu afuwa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima, ya bayyana asarar da aka yi saboda zanga-zangar #EndBadGovernance.

Kashim Shettima ya ce an yi asarar sama da Naira biliyan 300 a zanga-zangar #EndBadGovernance da aka gudanar a faɗin ƙasar nan cikin watan Agusta.

Shettima ya yi magana kan zanga zanga
Kashim Shettima ya ce an yi asarar N300bn sakamakon zanga-zanga Hoto: Kashim Shettima
Asali: Facebook

Mataimakin shugaban ƙasan ya bayyana hakan ne a fadar shugaban ƙasa da ke Abuja a ranar Talata, 5 ga watan Oktoban 2024, cewar rahoton jaridar Daily Trust.

Kara karanta wannan

Bayan hukuncin kotu, an bayyana dalilin Tinubu na sakin yaran Kano da aka kama

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kashim Shettima ya yi jawabin ne lokacin da yake magana a fadar shugaban ƙasa, Abuja, yayin da yake ƙarbar ƙananan yaran da suka shiga zanga-zangar bayan Shugaba Bola Tinubu, ya umarci a sake su.

Shettima ya yi batun asara saboda zanga-zanga

Shettima ya ce galibin asarar da aka yi a lokacin zanga-zangar ta shafi ƴan kasuwa ne.

Ya bayyana cewa duk da shaidun da ake da su a kan ƙananan yaran, shugaba Tinubu ya umarci a sake su saboda shugaba ne mai tausayi, rahoton Vanguard ya tabbatar da hakan.

"Ina yi muku nasiha, samari ka da ku bari a yi amfani da ku wajen tashe-tashen hankula da lalata dukiyoyin jama’a."
"An yi asarar sama da Naira biliyan 300 saboda zanga-zangar wacce ta shafi galibin ƴan kasuwa ne."

- Kashim Shettima

Shettima ya kuma yi kira ga gwamnoni da sauran jami'an gwamnati da su ɗora yaran a kan hanyar da za su zama masu amfani a cikin al'umma.

Kara karanta wannan

Kotu ta yanke hukunci kan yara masu zanga zanga da aka kama a a Arewa

Haɗarin da Kashim Shettima ya ke ciki

A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban majalisar dokokin jihar Borno, Abdulkarim Lawan, ya ce rayuwar mataimakin shugaban ƙasa Kashim Shettima na cikin haɗari.

Shugaban majalisar ya ce rayuwar Shettima na cikin haɗari ne sakamakon lalataccen jirgin shugaban ƙasa da yake amfani da shi wajen wakiltar Bola Tinubu a wajen taruka a faɗin duniya.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng