Sabuwar Kungiyar Yan Ta'adda na Raba Miliyoyi Domin Rudar Matasan Arewa

Sabuwar Kungiyar Yan Ta'adda na Raba Miliyoyi Domin Rudar Matasan Arewa

  • Rahotanni da suka fito daga jihar Sokoto na nuni da cewa an samu wata sabuwar kungiyar yan ta'adda da ke ɗaukar matasa
  • Kungiyar Lakurawa ta fito daga ƙasashen Mali, Libya da Nijar ta fara ta'addanci wajen sace sace a wasu yankunan Sokoto
  • Shugaban karamar hukumar Tagaza ya bayyana cewa a yanzu haka yan ta'addar sun shiga dazuka a ƙananan hukumomi biyar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Sokoto - An samu bullar sabuwar kungiyar yan ta'adda da ake kira Lakurawa a wasu yankunan jihar Sokoto.

Rahotanni na nuni da cewa yan ta'addar sun fito ne daga kasashen Mali, Libya da Nijar kuma sun fara ɗaukar matasa.

Kara karanta wannan

Sojojin sama sun yi ajalin 'yan ta'adda da ke kokarin hana gyara lantarkin Arewa

Sokoto
Yan ta'adda na daukar matasa a Sokoto. Hoto: Legit
Asali: Original

Jaridar Daily Trust ta wallafa cewa hukumomi a jihar sun fara tattaunawa kan yadda za su fuskanci sabon ƙalubalen.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yan ta'adda na raba miliyoyi ga matasa

Wata kungiyar yan ta'adda mai suna Lakurawa da ta kunno kai a Sokoto ta fara raba N1m ga matasa domin shiga cikinta.

Shugaban karamar hukumar Tagaza, Isa Salihu ya bayyana cewa suna ba matasan makudan kudin ne domin su rude su.

Lakurawa sun fara ta'addanci a Sokoto

An ruwaito cewa kungiyar Lakurawa ta kashe sojoji hudu a wani hari da ta kai a kan hanyar Gudu.

Haka zalika kungiyar ta fara tilasta mutane biyan Zakka, kuma yan kungiyar sun sace N2m wajen wani mai shago tare da kwace wata mota.

Kokarin gwamnati wajen yakar Lakurawa

Mataimakin gwamnan jihar Sokoto ya ce lamarin ya fito alhalin jihar na fama da matsalar yan bindiga masu garkuwa da mutane.

Kara karanta wannan

Bayan masifar yan bindiga, wasu gungun miyagu daban sun sake bulla a Sokoto

Idris Gobir ya tabbatar da cewa suna tattaunawa da jami'an tsaro domin ganin yadda za su fuskanci matsalar.

Ya kuma kara da cewa yan ta'addar suna dauke da makamai kuma sun fara hada kai da yan bindiga wajen kai hare hare.

Sojoji sun kashe yan ta'addan ISWAP

A wani rahoton, kun ji cewa sojojin saman Najeriya sun kai farmaki kan yan ta'addar ISWAP a jihar Borno a cikin 'yan kwanakin nan.

An tabbatar da cewa sojojin saman sun hallaka yan kungiyar ISWAP kimanin 50, ciki har da babban jagoransu mai suna Bashir Dauda.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng