Tsohon Gwamna a Najeriya Ya Ce Ba Zai Ji Haushin Matarsa Ba Ko Tana Neman Maza

Tsohon Gwamna a Najeriya Ya Ce Ba Zai Ji Haushin Matarsa Ba Ko Tana Neman Maza

  • Tsohon gwamnan Anambra, Peter Obi ya ce shi da matarsa mutu ka raba amma ba abin da zai sa ya danƙara mata saki
  • Dan takarar shugaban ƙasa na LP a 2023 ya ce ko da matarsa za ta ci amanarsa ta hanyar neman maza, ba zai sake ta ba
  • Peter Obi ya faɗi haka ne a wata hira da ya yi kwanan wadda ta haddasa ce-ce-ku-ce a kafafen sada zumunta na zamani

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Anambra - Ɗan takarar shugaban ƙasa a inuwar jam'iyyar LP a zaɓen 2023, Peter Obi ya haddasa ce-ce-ku-kuce da ya yi wata magana game da rayuwarsa ta aure.

Obi, tsohon gwamnan jihar Anambra ya ce ko da a ce ya kama matarsa da cin amana ba zai taɓa danƙara mata saki ba.

Kara karanta wannan

Bayan hukuncin kotu, an bayyana dalilin Tinubu na sakin yaran Kano da aka kama

Peter Obi da matarsa.
Peter Obi ya ce ba zai taba sakin matarsa ko kara aure ba har abada Hoto: Mr. Peter Obi
Asali: Facebook

Peter Obi ya faɗi haka ne a wata hira da aka yi da shi kwanan nan a shafin Youtube na The Honest Bunch.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Peter Obi ya ce aurensa mutu ka raba

A yayin tattaunawar, Obi ya bayyana da kwarin gwiwa cewa ko da matarsa ta shekara 32, Margaret Usen, ta ci amanarsa ba zai yanke hukuncin sakinta ba.

"Ko me matata za ta yi yau, ba zan taba rabuwa da ita ba, ko da za ta dauki bindiga ta nuna za ta harbe ni ba zan sake ta ba.
"Matukar ina raye daga nan har abada ba zan taɓa kara aure ba, ita kaɗai ce matata," in ji Obi.

Fitaccen ɗan siyasar ya nuna cewa ya rufe ƙofa indai a batun aure ne, inda ya ce ba zai taɓa ƙara aure ba ko da kuwa ya rabu da matarsa.

Kara karanta wannan

Gwamnati ta sauya tsarin shiga shekarun shiga jami'a kwana 1 da nada Minista

"Ko neman maza take yi babu ruwana" - Obi

Tsohon gwamnan ya ce duk abin da matarsa za ta yi, ba zai taɓa ɓata masa rai ba balle har ya furta mata kalmar saki.

"Na rufe ƙofa, matukar dai ina raye ita ce kaɗai matata, ba ruwana da ƙara aure ko kiwa ƙulla alaka da wata mata. Duk abin da matata take so ta yi, ba zai ɓata mani rai ba.
"To me ma zai ɓata mun rai? Idan tana cin amanata da wani, matsalarta ce, ba ruwana, iyaka dai mutane su ce Peter Obi mutumin kirki ne amma ya auri mace sai a hankali, shikenan."

Obi ya yi magana kan limamin Masallacin Abuja

A wani rahoton, kun ji cewa tsohon dan takarar shugaban kasa a inuwar LP, Peter Obi ya taya sabon limanin masallacin Abuja fatan alheri.

Dan siyasar ya bayyana nadin da wata manuniya kan jajircewa da jagorancin Iliyasu Usman ta bangaren addini.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262