Gwamna Ya Fadi Shirin Tinubu domin Rage Talauci a Najeriya
- Gwamnan jihar Kaduna, Malam Uba Sani ya yaba da shirin da Bola Tinubu ya fito da shi domin tallafawa masu ƙananan sana'o'i
- Uba Sani ya bayyana cewa shugaban ƙasan mai kunnen basira ne kuma ya ƙudiri aniyar ganin ya kawar da talauci a Najeriya
- Ya nuna cewa shirin an tsara shi ne domin amfanin masu ƙananan sana'o'i da masana'antu ta yadda tattalin arziƙin jihohi da na ƙasa baki ɗaya zai bunƙasa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Kaduna - Gwamnan jihar Kaduna, Uba Sani, ya yi magana kan shirin shugaban ƙasa Bola Tinubu na rage talauci a Najeriya.
Gwamna Uba Sani ya ce shugaba Bola Tinubu ya ƙudiri aniyar kawar da talauci a Najeriya.
Uba Sani ya bayyana haka ne a wajen wani taron wayar da kan jama’a game da shirin bayar da tallafin kuɗi na Naira biliyan 200 na shugaban ƙasa domin masu ƙananan sana'o'i, cewar rahoton jaridar The Nation.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamnatin tarayya tare da haɗin gwiwar bankin masana’antu suka shirya a taron Kaduna a ranar Talata.
Gwamna Uba Sani ya yabawa shirin Tinubu
Gwamna Uba Sani ya samu wakilcin mai ba shi shawara na musamman kan harkokin tattalin arziƙi, Mista Ibrahim Muhammad.
Ya ce shirin an tsara shi ne domin bunƙasa tattalin arziƙin Najeriya ta hanyar ƙarawa ƴan kasuwa na cikin gida ƙarfi.
"Wannan gagarumin shiri na shugaban kasa hujja ce da ke nuna cewa shugaba Tinubu jagora ne mai sauraren koken mutanensa."
"Ta hanyar waɗannan shirye-shiryen, za a farfaɗo da ƙananan ƴan kasuwa da masana'antu, wanda hakan zai amfani tattalin arziƙin jihohi da ƙasa baki ɗaya."
-.Gwamna Uba Sani
Tinubu ya magantu kan tsadar rayuwa
A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya yi magana kan tsadar rayuwar da ake fama da ita a ƙasar nan.
Tinubu ya amince cewa akwai tsadar rayuwa a ƙasar nan, inda ya tabbatarwa ƴan Najeriya cewa gwamnatinsa na ɗaukar matakai na rage wahalhalu da farfaɗo da tattalin arziƙin ƙasar nan.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng