Ambaliya: Buhari Ya Dura Borno, Ya Fadi Dalilin Rashin Zuwa Jaje a kan Lokaci

Ambaliya: Buhari Ya Dura Borno, Ya Fadi Dalilin Rashin Zuwa Jaje a kan Lokaci

  • Tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ya dura jihar Borno sama da wata daya bayan ambaliyar ruwa da ta laƙume rayuka
  • Muhammadu Buhari ya gana da manyan shugabannin jihar Borno yayin da ya musu jaje kan mummunar ambaliyar ruwa
  • Manyan yan siyasa karkashin jagorancin gwamna Babagana Umara Zulum ne suka karbi tsohon shugaban kasar a filin jirgin sama

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Borno - Tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kai ziyara jihar Borno domin jaje kan ambaliyar ruwa.

A watan Satumba da aka yi ambaliyar, Muhammadu Buhari ta tura Sheikh Isa Ali Pantami ya wakilce shi.

Buhari
Buhari ya je jaje Maiduguri bayan ambaliyar ruwa. Hoto: Garba Shehu
Asali: Facebook

Tsohon hadimi a fadar shugaban kasa, Garba Shehu ne ya wallafa wuraren da Muhammadu Buhari ya ziyarta a Maiduguri a shafinsa na X.

Kara karanta wannan

Mataimakin shugaban Majalisar Dattawa ya yi rashin hadimi, wani ɗan sanda ya rasu

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ambaliyar ruwa a Maiduguri

A watan Satumba da ya wuce aka yi wata mummunar ambaliyar ruwa a birnin Maiduguri na jihar Borno.

Legit ta ruwaito cewa ambaliyar ruwan ta jawo asarar rayuka da dukiya yayin da al'umma da dama suka rasa yan uwa da gidajen zama.

Muhammadu Buhari ya ziyarci Borno domin jaje

Tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ziyarci jihar Borno domin jaje kan ambaliyar ruwa da ta faru a Satumba.

Gwamna Babagana Umara Zulum, Sanata Ali Ndume na cikin manyan yan siyasa da suka tarbi shugaba Buhari a filin jirgin sama.

Muhammadu Buhari ya ziyarci fadar shehun Borno, Mai martaba Abubakar Ibn Umar Garba Al-Amin El-Kanemi domin jaje.

"Tsohon shugaban kasar ya tafi wani hutu na musamman a lokacin da ambaliyar ruwan ta faru.
Saboda haka sai yanzu ya zo da kansa domin mika jaje ga shehun Borno, gwamnatin jihar Borno da dukkan mutanen jihar kan ambaliyar ruwan"

Kara karanta wannan

Rashin lantarki: An fara haɗa alkaluman asarar Arewa, za a nemi diyya daga Tinubu

- Garba Shehu

Gwamna ya raba tallafin ambaliyar ruwa

A wani rahoton, mun ruwaito muku cewa gwamnan jihar Jigawa, Umar Namadi ya waiwayi mutanen da ambaliyar ruwa ta ritsa da su a daminar bana.

Mai girma Gwamnan ya amince a fitar da N315.5m domin rabawa ga mutane 15,775 da ke a sansanonin ƴan gudun hijira a inda lamarin ya shafa.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng