Yan Kasuwa Sun Dage Shigo da Fetur daga Kasar Waje Zai Fi Man Dangote Arha

Yan Kasuwa Sun Dage Shigo da Fetur daga Kasar Waje Zai Fi Man Dangote Arha

  • Yan kasuwa sun tsaya a kan bakarsu na cewa fetur da za su dauko daga kasar waje ya fi wanda ake sayarwa a kasar nan sauki
  • Kungiyar ‘Petroleum Products Retail Outlets Owners Association of Nigeria (PETROAN)’ ta ce fetur zai shigo kasar nan kafin watan Disamba
  • Yan kasuwa sun kuma yi martani kan zargin da matatar Dangote ta yi masu na sayo gurbataccen fetur da ya fi wanda ta ke samarwa arha

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar LagosKungiyar yan kasuwar man fetur ta Petroleum Products Retail Outlets Owners Association of Nigeria (PETROAN) ta ce za ta ci gaba da sayo fetur a kasashen waje.

Kara karanta wannan

PDP ta fadi kullin da zai kori APC daga fagen siyasa bayan zaben 2027

Jami’in hulda da jama’a PETROAN na kasa, Dr. Joseph Obele ya bayyana cewa dole ce ta sa ba za su rika sayen fetur daga cikin kasar nan ba.

Fetur
Za a shigo da fetur daga kasar waje Hoto: Bloomberg/Contributor
Asali: Getty Images

Jaridar Vanguard ta ruwaito kungiyar ta bayyana cewa fetur da za ta dauko daga kasashen ketare zai fi wanda ake sayarwa a kasar nan arha.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Za a shigo da man fetur Najeriya

Jaridar Punch ta tattaro cewa yan kasuwa sun ce an dauki matakin da zai ba su damar shigo da fetur kasar nan kafin watan Disamba.

Kungiyar ta na ganin matakin da ta dauka zai saukaka farashin man fetur, sai dai ba ta yi bayani ko za a rage farashin da ta ke sayarwa yan kasa ba.

Yan kasuwar fetur sun musanta zargin Dangote

Kungiyar Petroleum Products Retail Outlets Owners Association of Nigeria ta musanta zargin da matatar Dangote ta yi masu na kokarin shigo da gurbataccen fetur.

Kara karanta wannan

Band A: Masu samun wutar awa 20 a rana sun gaji, sun kai kuka wajen Tinubu

Kamfanin Pinnacle Oil and Gas Limited ya kuma musanta cewa ya na gyara gurbataccen fetur ga wasu kamfanonin ketare a cikin gida Najeriya.

Matatar Dangote ta fadi farashin fetur

A baya mun ruwaito cewa matatar mai ta Dangote ta musanta zargin da yan kasuwa ke yi na cewa fetur da ake daukowa da kasashen waje ya fi wanda ta ke fitarwa sauki.

An samu masu zargin matatar Dangote da sayar da fetur da tsada ga yan kasar nan duk da cewa ana sayen danyen fetur ne daga Najeriya kuma ana tace shi a jihar Legas ba kasar waje ba.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.