Gwamnatin Equatorial Guinea Ta Dauki Darasi, An Cafke Jami'in da Ya Yi Lalata da Mata 400

Gwamnatin Equatorial Guinea Ta Dauki Darasi, An Cafke Jami'in da Ya Yi Lalata da Mata 400

  • Kasar Equatorial Guinea ta fusata da yadda daya daga cikin jami'an gwamnatin ya jawo mata abin kunya a idon duniya
  • An kama Darakta Janar na hukumar binciken kudi na kasar, Baltasar Engonga da bidiyon lalata da mata sama da 400
  • Gwamnatin ta dauko aikin sanya kyamarori a ofisoshin kasar domin sa ido a kan masu irin wannan danyen aiki da dakile shi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Equatorial Guinea - Mataimakin shugaban kasar Masar Equatorial Guinea, Teddy Nguema ya bayyana matakin da gwamnati za ta dauka bayan samun jami’inta da lalata da mata akalla 400.

An kama Darakta Janar na hukumar binciken kudi na kasar, Baltasar Engonga, da bidiyon lalata da wasu mata sama da 400, daga cikin su akwai wadanda ke auren manya a kasar.

Kara karanta wannan

Bayan masifar yan bindiga, wasu gungun miyagu daban sun sake bulla a Sokoto

Guinea
Za a sa kyamarori a ofisoshin gwamnatin Equatorial Guinea Hoto: Baltasar Ebang Engonga
Asali: Facebook

Jaridar Punch ta tattaro cewa cewa gwamnatin Equatorial Guinea ta ce ba za ta zuba idanu ana aikata irin wannan danyen aiki a ofisoshin gwamnati ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ana binciken jami’in gwamnatin Equatorial Guinea

BBC Pidgin ta wallafa cewa mahukunta a Equatorial Guinea sun fara binciken Baltasar Engonga da sauran wadanda ake zargi da badala bayan samun bidiyo sama da 400.

Daga cikin matakan da hukumomi su ka dauka akwai dakatar da jami’in gwamnatin yayin da ake ci gaba da binciken batun.

Za a sa kyamarori a ofisoshin Equatorial Guinea

Gwamnati ta bayyana shirinta na zuba kyamarori a ofisoshin dukkanin ma’aikatan kasar domin dakile ayyukan badala a tsakanin ma’aikatan kasar.

Mataimakin shugaban kasar, Equatorial Guinea, Teddy Nguema ya bayyana cewa duk wanda aka kama a kan kyamara ya na aikata ba daidai ba zai fuskanci shari’a.

Kara karanta wannan

Band A: Masu samun wutar awa 20 a rana sun gaji, sun kai kuka wajen Tinubu

Tinubu ya shilla Equatorial Guinea

A baya mun ruwaito cewa fadar shugaban Najeriya ta bayyana shirin shugaba Bola Ahmed Tinubu na tafiya kasar Equatorial Guinea inda zai shafe akalla kwanaki uku a ziyarar aiki.

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya samu rakiyar manya daga cikin jami'an gwamnatinsa da su ka hada da ministan harkokin kasashen waje, Ambasada Yusuf Tuggar da wasu ministocinsa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.