Kotu Ta Yanke Hukunci kan Yara Masu Zanga Zanga da Aka Kama a Arewa

Kotu Ta Yanke Hukunci kan Yara Masu Zanga Zanga da Aka Kama a Arewa

  • Babbar kotun tarayya mai zama a Abuja ta saki kananan yaran da aka kama a Kano lokacin zanga-zangar adawa da tsadar rayuwa
  • Mai shari'a Obiora Egwuatu ya kori ƙarar da ake tuhumar yaran bayan Antoni Janar na ƙasa (AGF) ya buƙaci ayi watsi da shari'ar
  • Wannan na zuwa ne sa'o'i kaɗan bayan shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya ba da umarnin a sake su bayan korafi daga kusan ko ina

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - Wata babbar kotun tarayya da ke zama Abuja ta kori karar da ake tuhumar yaran da aka kama a Kano lokacin zanga-zangar #EndBadGovernance.

Mai shari’a Obiora Egwuatu ya yi fatali da karar ne biyo bayan bukatar da M.D Abubakar, lauyan Antoni Janar na tarayya (AGF) ya gabatar a kotun.

Kara karanta wannan

2027: Tsohon hadimin shugaban ƙasa ya faɗi ma'anar sunan 'T-Pain' da ake kiran Tinubu

Yaran Kano.
Babbar kotun tarayya ta saki yaran Kano da yan sanda suka gurfanar a Abuja Hoto: Ayman Ado
Asali: Facebook

AGF ya buƙaci dakatar da shari'ar yara

Kamar yadda The Cable ta ruwaito, AGF ta hannun lauyansa ya bukaci karɓe karar da kuma dakatar da ita kamar yadda kundin tsarin mulki ya ba shi dama.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Lauyan AGF ya ce:

"Muna bukatar karɓe ragamar shari'ar tare da dakatar da ita kamar yadda kundin tsarin mulkin Najeriya ya tanada."

Lauyoyin yaran sun amince da buƙatar AGF

A nasa ɓangaren lauyan ƙananan yaran, Femi Falana, wanda ke wakiltar waɗanda ake tuhuma na 1 zuwa na 50, ya ce ba su da jayayya da wannan buƙata.

"AGF yana da karfin ikon karɓe ƙara a kowane mataki kuma ya yi amfani da damarsa wajen dakatar da shari'ar gaba ɗaya," in ji Falana.

Ɗayan lauyan da ke kare sauran yaran da ake tuhuma, Hamza Kyari, ya amince da buƙatar Antoni Janar na dakatar da ƙarar.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu ya dauki mataki kan yaran da aka tsare saboda zanga zanga

Kotu ta yanke hukunci sakin yaran Kano

Daga nan sai Mai Shari'a Obiora Egwuatu na babbar kotun tarayya ta kori ƙarar gaba ɗaya, ma'ana dai an saki yaran kenan, kamar yadda Daily Trust ta kawo.

Wannan na zuwa ne sa’o’i kadan bayan shugaban kasa Bola Tinubu ya umurci AGF da hukumomin tsaro su saki dukkan kananan yara da ake tsare da su saboda zanga-zangar.

Lauyan yaran da ake tuhuma ya magantu

A wani rahoton, kun ji cewa Lauya mai kare yaran da aka kama a lokacin zanga zangar tsadar rayuwa, Hamza Nuhu Dantani ya yi karin haske kan halin da ake ciki.

Barista Nuhu Hamza Dantani ya yi zargin cewa ba a bi ƙa'ida wajen kama yaran ba kuma an karya doka wajen gabatar da su a kotu.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262