Bayan Masifar Yan Bindiga, Wasu Gungun Miyagu Daban Sun Sake Bulla a Sokoto

Bayan Masifar Yan Bindiga, Wasu Gungun Miyagu Daban Sun Sake Bulla a Sokoto

  • Al'ummar Sokoto sun sake cin karo da wata matsala mai girma sakamakon bullar wasu miyagun yan ta'adda daban a jihar
  • Gwamnatin jihar ta tabbatar da bullar wasu masu alaka ta addini da ake kira Lakurawas alhali ana fama da yan bindiga
  • Mataimakin gwamnan jihar, Idris Gobir shi ya tabbatar da haka inda ya ce suna nan a kananan hukumomi har guda biyar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Sokoto - Yayin da jihar ke fama da matsalar yan bindiga, gwamnatin Sokoto ta ce an samu bullar wasu miyagu.

Mataimakin gwamnan jihar, Idris Gobir ya ce wasu yan ta'adda da ake kira Lakurawas sun bulla a jihar.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Tinubu ta fara shirin janye zarge zarge kan yara 32 a gaban kotu

Wata kungiyar yan ta'adda ta ɓulla a Sokoto
Gwamnatin Sokoto ta tabbatar da bullar wasu miyagu LAKURAWAS a jihar. Hoto: Ahmed Aliyu.
Asali: Facebook

Sabuwar kungiyar ta'adda ta bulla a Sokoto

Gobir ya bayyana haka yayin karbar bakuncin daliban Kwalejin Tsaro ta kasa da suka kai ziyara a jihar, cewar Vanguard.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mataimakin gwamnan ya ce kungiyar tana da alaƙa da addini kuma suna dauke da muggan makamai tare da su.

Har ila yau, Gobir ya ce bincike ya tabbatar da cewa sun fara ayyukansu a ƙananan hukumomi biyar da ke jihar, Tribune ta ruwaito.

Ya nuna damuwa kan lamarin, ya ce hakan ya zo a daidai lokacin da jihar ke fama da matsalolin yan bindiga.

Gwamnatin Sokoto ta magantu kan dakile rashin tsaro

"Gwamnatin jiha na yin haɗaka da jami'an tsaron Gwamnatin Tarayya domin dakile matsalolin tsaro da al'umma ke fama da su."

- Idris Gobir

A bangarensa, shugaban tawagar, Air Vice Marshal Titus Zuwahu Dauda ya ce an kirkiri Kwalejin ne a shekarar 1992.

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun sake kai mummunan hari, sun kashe uba da yaƴansa 2

Zuwahu ya ce kwalejin na zabar jami'an tsaro daga sojoji da yan sanda da sauran hukumomin tsaro domin ba su horaswa ta musamman.

Yan bindiga sun kafa tuta a Taraba

A baya, kun ji cewa wasu yan bindiga sun mamaye wani tsauni a karamar hukumar Zing da ke jihar Taraba inda suka kafa jar tuta.

Miyagun sun taba zuwa wannan yanki a daidai wannan lokaci a bara kafin jami'an tsaro su fatattake su a iyakar Taraba da Adamawa.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.