Gwamnatin Tinubu Ta Yi Magana Kan Yiwuwar Dawo da Tallafin Man Fetur a Najeriya
- Ministan kudi da tattalin arziki, Wale Edun ya karbi baƙuncin sabuwar karamar ministar da Tinubu ya naɗa a ma'aikatar ranar Litinin
- Edun ya ce ba gudu ba ja da baya kan batun cire tallafin mai da tsame hannun gwamnati a canjin Dala zuwa Naira
- Ya ce nan gaba ƴan Najeriya za su amfama da manufofin shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu kan cire tallafin mai
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja - Ministan kudi da harkokin tattalin Arziki, Wale Edun, ya ce babu gudu babu ja da baya game da manufofin shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu.
Mista Edun ya tabbatar da cewa shugaban ƙasa ba zai janye kudirinsa na cire tallafin man fetur da canza tsarin canjin kuɗi ba.
Daily Trust ta ce ya faɗi hakan ne a lokacin da ya karbi bakuncin sabuwar ƙaramar ministar kudi, Doris Uzoka Anite a hedikwatar ma’aikatar ranar Litinin a Abuja.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamnatin Tinubu tace tallafin mai ya tafi kenan
"A yanzu dai farashin canjin Dala ya dogara ne da kasuwa, haka kuma yanayin kasuwa ne ke yanke farashin fetur, waɗannan abubuwa ne da tuntuni aka fara Tinubu ke aiwatarwa."
"A matsayin waɗanda aka ɗora mana alhakin kula da ma'aikatar tattali arziki, dole mu jajirce wajen aiwatar da manufofin shugaban ƙasa tare da samar da aiki da rage raɗaɗin talauci.
"Muna farin cikin samun karamin minista wanda za ta aimaka wajen aiwatar da manufofin shugaban ƙasa."
- Wale Edun.
Manufofin Tinubu za su kawo cigaban ƙasa
Mista Edun ya kara da cewa alamu sun nuna tsare-tsaren Tinubu za su kawo ci gaba da nasara a ƙasar nan gaba, rahoton Punch.
A jawabinta, karamar ministar kudi ta jaddada kudirin aiki tare da masu ruwa da tsaki a bangarorin masu zaman kansu da na gwamnati don farfafo da tattalin arziki.
Gwamnatin Tinubu ta rabawa mutane tallafi
A wani rahoton, kun ji cewa gwamnatin tarayya ta ce zuwa yanzu ta turawa ƴan Najeriya miliyan 25 har N25,000 domin rage raɗaɗin halin da ake ciki.
Ministan kudi da harkokin tattalin arziki, Wale Edun ne ya bayyana haka jim kaɗan bayan taron majalisar tattalin arziƙi NEC.
Asali: Legit.ng