"Za a Zage Ku," Abin da Tinubu Ya Faɗawa Sababbin Ministoci bayan Rantsar da Su

"Za a Zage Ku," Abin da Tinubu Ya Faɗawa Sababbin Ministoci bayan Rantsar da Su

  • Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya faɗawa sababbin ministoci cewa su kwana da shirin ƴan Najeriya za su zage su saboda halin da ake ciki
  • Shugaban ƙasar Najeriyan ya roki sababbin ministocin su maida hankali kan ayyukan da aka ɗora masu na ceto ƙasar nan
  • Wannan na zuwa ne bayan ministocin sun karɓi rantsuwar kama aiki a fadar shugaban ƙada da ke Abuja ranar Litinin, 4 ga Nuwamba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

State House, Abuja - Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya faɗawa sababbin ministoci bakwai cewa su dhirya shan shagi da hantara saboda sun shiga gwamnati.

Bola Tinubu ya faɗi haka ne a wurin bikin rantsar da ministocin a fadar shugaban ƙasa da ke Abuja ranar Litinin, 4 ga watan Nuwamba, 2024.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Tinubu ta yi magana kan yiwuwar dawo da tallafin man fetur a Najeriya

Tinubu tare da ministoci.
Shugaba Tinubu ya buƙaci sababbin ministoci su jajirce wajen sauke nauyin da ya rataya a kansu Hoto: @KashimSM
Asali: Twitter

Me zai sa a zagi sabbabin ministocin?

Premium Times ta ruwaito Tinubu na shaidawa ministocin cewa su kwana da shirin shan zagi daga wasu ƴan Najeriya saboda sun shiga gwamnatinsa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"A yanzu kun shigo layi waɗanda ake zagi da suka amma ka da ku damu kanku, ku jajirce wajen aikinku kawai."

Shugaban ƙasar ya ce ministocin sun shigo gwamnatinsa a daidai lokacin da Najeriya ke fuskantar kalubalen tattalin arziki da sauran matsaloli kamar rashin tsaro.

Bola Tinubu ya taya su murnar fara aiki

"Ina kara taya sababbin minsitocin da aka rantsar murna, ina taya ku murna da kuma gode maku bisa yadda ku ka amince za ku yi wa ƙasa hidima.
"Ba abu ne mai sauƙi ba samun waɗanda za su sadaukar da kansu, su ba da lokacinsu domin yi wa kasa hidima duk da ana cikin ƙalubale.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu ya yi sababbin naɗe naɗe a hukumar INEC ta ƙasa, an samu bayani

- Bola Tinubu.

Waɗanda suka karbi ranstuwar kama aiki sun hada da Nentawe Yilwatda, Muhammadu Dingyadi da Bianca Odumegu-Ojukwu.

Ragowar su ne: Jumoke Oduwole, Idi Maiha, Yusuf Ata da Suwaiba Ahmad.

Tinubu ya naɗa kwamishinoni a INEC

A wani rahoton, kun ji cewa Bola Ahmed Tinubu ya yi sababbin naɗe-naɗe a hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa watau INEC..

Tinubu ya naɗa Abdulrazak Yusuf Tukur a matsayin kwamishinan INEC mai kula da shiyyar Arewa maso Yammacin Najeriya da kwamishinan zaɓe a Ogun.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262