Shugaba Tinubu Ya Yi Sababbin Naɗe Naɗe a Hukumar INEC Ta Ƙasa An Samu Bayani
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
State House, Abuja - Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya yi sababbin naɗe-naɗe a hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa watau INEC.
Bola Tinubu ya naɗa Abdulrazak Yusuf Tukur a matsayin kwamishinan INEC mai kula da shiyyar Arewa maso Yammacin Najeriya.
Daily Trust ta ce Tinubu ya kuma ɗauko wani lauya Saseyi Feyijimi Ibiyemi, ya naɗa shi a matsayin wanda zai maye gurbin marigayi kwamishinan zabe na jihar Ogun.
Mai ba shugaban ƙasa shawara na musamman kan harkokin yaɗa labarai da dabaru, Bayo Onanuga ne ya bayyana hakan a wata sanarwa yau Litinin.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya ce Abdulrazak Yusuf ya kammala digirinsa na farko a jami'ar Bayero da ke Kano (BUƘ), sannan ya yi diflomar digiri na biyu a jami'ar Bradford ta ƙasar Ingila.
Bugu da ƙari, kakakin shugaban ƙasar ya ve Abdulrazak ya gama digiri na biyu a jami'ar Leeds duk a ƙasar Ingila.
Ya fara aiki da INEC a shekarar 1999 a matsayin mataimakin babban jami’in gudanarwa sannan ya zama daraktan ayyuka da dabaru na zabe.
Karin bayani na nan take...
Asali: Legit.ng