Kungiyar Arewa Ta Maka Kafar Arewa24 a gaban Kotu, Dalilai Sun Bayyana
- Kungiyar masu kafafen yada labarai ta NBMOA ta sake maka tashar nan ta Arewa24 a gaban kotu bisa zargin aiki babu lasisi
- Shugaban kwamitin amintattu na kungiyar Alhaji (Dr.) Ahmed Tijjani Ramalan ya bayyana cewa Arewa24 ta zama barazana ga Arewa
- Wannan ba shi ne karon farko da kungiyar masu kafafen yada labaran da ke Arewacin kasar nan ke maka Arewa24 a gaban kotu ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano – Kungiyar masu kafafen yada labarai ta Northern Broadcast Media Owners Association (NBMOA) ta maka tashar talabijin Arewa24 da wasu guda bakwai a gaban kotu.
Kungiyar NBMOA ta dauki matakin ne bisa zargin Arewa24 da sauran kafafen bisa zargin gudanar da ayyukansu ba tare da lasisin da ya dace ba.
Jaridar Vanguard ta wallafa cewa tuni aka shigar da karar gaban babbar kotun tarayya da ke Abuja karkashin mai shari’a Omotosho.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Su wa NBMOA ta maka a kotu?
Jaridar Independent Newspapaper ta wallafa cewa kungiyar masu gidajen kafafen yada labarai a Arewacin Najeriya sun shigar da Arewa24 kara a gaban kotu.
Sauran wadanda NBMOA ke zargi da take doka sun hada da hukumar kula da kafafen yada labarai (NBC), Ma’aikatar yada labrai da wayar da kan jama’a ta kasa da hukumar kula da tallace tallace ta kasa (ARCON).
Suaran sun hada da hukumar kare masu saye, MIPAN, MultiChoice, Startimes da dai wasu hukumomin da ke da alhakin kula da ayyukan kafafen yada labarai.
Dalilin maka NBMOA na kai Arewa24 kotu
Kungiyar masu kafafen yada labarai reshen Arewacin Najeriya ta bayyana dalilinta na shigar da kara kotu a kan kafar tabijin ta Arewa24 da wasu guda bakwai a gaban kotu.
A sanarwar da shugaban kwamitin amintattu na Kungiyar Alhaji (Dr.) Ahmed Tijjani Ramalan ya fitar, ya ce ana zargin Arewa24 ta zama babbar barazana ga masu kafafen yada labarai da al’umar da ke kallonsu.
Masu kafafen yada labarai sun kai Arewa24 kotu
A wani labarin kun ji cewa kungiyar masu kafafen yada labarai ta Arewa (NBMOA) ta kai ƙarar tashar Arewa24 a gaban kotu bisa zargin cewa su na lalata al'adar Malam Bahaushe.
Kungiyar ta zargi tashar da gudanar da shirye-shiryen da suka ci karo da al'ada da addinin al'ummar Hausawa inda ta nemi hukumomi da su gaggauta dakatar da harkokin tashar.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng