Band A: Masu Samun Wutar Awa 20 a Rana Sun Gaji, Sun Kai Kuka wajen Tinubu

Band A: Masu Samun Wutar Awa 20 a Rana Sun Gaji, Sun Kai Kuka wajen Tinubu

  • Yan kasar nan da ke kan tsarin 'band A' na wutar lantarki sun fara kokawa tare da neman daukin gwamnatin Bola Tinubu
  • An raba masu amfani da hasken lantarki a Najeriya zuwa aji daban-daban, kuma yan 'band A' ke samun wutar akalla awa 20
  • Sai dai sun fara kukan farashin da kamfanonin hasken lantarki ke karba daga masu amfanuwa da wutar a wasu yankuna

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abuja - Mazauna wasu sassan babban birnin tarayya Abuja da ke tsarin samun hasken lantarki na 'band A' sun fara neman daukin gwamnatin tarayya.

Yan kasar nan da ke bisa tsarin 'band A' na samun hasken wutar lantarki kan sha wuta ta akalla awanni 20, kuna za su rika biyan N209.5 a kan kowace kilowatt a cikin sa'a guda.

Kara karanta wannan

Matsala ta kunno kai a Kano, takardun Naira sun fara ƙaranci a hannun jama'a

Tinubu
Mazauna Abuja sun koka kan tsadar lantarki Hoto: Bayo Onanuga
Asali: Facebook

Jaridar Vanguard ta tattaro cewa sai dai duk da hasken lantarki da ake samu, mazauna Lugbe, Area 10, da Apo sun bayyana cewa kudin lantarkin zai fi karfinsu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An mika koken farashin lantarki ga Tinubu

Jaridar Punch ta wallafa cewa wata da ke zaune a yankin Lugbe da ke Abuja, Amen Odigie ta ce ta kan biya kudin wuta akalla N30,000 a dakunanta biyu duk wata.

Ta bayyana cewa albashin da ta ke samu ba zai isa ta tafiyar da rayuwarta yadda ya kamata ba saboda yadda farashin komai ya yi tashin gwauron zabo.

An roki Tinubu kan rage kudin wutar lantarki

Mazauna sassan babban birnin tarayya Abuja sun bukaci gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ta tausaya masu wajen rage farashin wutar lantarki.

Mutanen Apo, Area 10 da Lugbe sun ce duk da ana samun isasshen hasken wutar lantarki a a kullum, amma akwai yiwuwar su gaza biyan kudin.

Kara karanta wannan

Uwargidan Tinubu, Ribadu za su jagoranci taron addu'a kan matsin rayuwa

Ministan Tinubu ya ba shawara kan kudin wuta

A wani labarin kun ji cewa Ministan makamashi, Adebayo Adelabu ya shawarci yan kasar nan a kan yadda za su rika biyan kudin wutar lantarki da zai dace da abin da su ke samu.

Ministan ya shawarci yan Najeriya da kar su sake su biya sabon kudin wutar lantarki da aka yanke masu matukar ba a kawo hasken wutar da ya dace da sabon farashin ba.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.