Shugaba Tinubu Ya Dauki Mataki kan Yaran da Aka Tsare saboda Zanga Zanga
- Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya umarci a gaggauta sakin yaran da aka tsare saboda zanga-zangar #EndBadGovernance
- Ministan yaɗa labarai da wayar da kan jama'a, ya bayyana hakan ga manema labarai a ranar Litinin, 4 ga watan Nuwamban 2024
- Mohammed Idris Malagi ya kuma bayyana cewa an kafa kwamitin da zai binciki kamu da tsare yaran da aka yi tun kwanaki
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Shugaban ƙasa Bola Tinubu, ya yi magana kan yaran da aka tsare tare da gurfanar da su a gaban kotu saboda zanga-zanga.
Shugaba Bola Tinubu ya bayar da umarnin a gaggauta sakin duk yaran da aka kama waɗanda suke fuskantar shari'a a gaban kotu bisa zarginsu da hannu a zanga-zangar #EndBadGovernance.
Ministan yada labarai da wayar da kan jama’a na ƙasa, Mohammed Idris ne ya bayyana hakan a lokacin da yake zantawa da manema labarai a fadar shugaban ƙasa da ke Abuja, cewar rahoton jaridar Vanguard.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Tinubu ya ba da umarni kan yaran da aka tsare
Shugaba Tinubu ya kuma umarci ministan jin ƙai da rage talauci da ya kula da ƙananan yaran.
Mohammed Idris ya bayyana cewa shugaban ƙasa ya umarci Antoni Janar na tarayya, Lateef Fagbemi, ya gaggauta fara bin hanyar tabbatar da sakin ƙananan yaran, rahoton jaridar Daily Trust ya tabbatar.
"Shugaban ƙasa ya umarci a saki dukkanin ƙananan yaran tare da sada su da iyalansu a ko'ina suke a ƙasar nan."
"An kafa kwamiti wanda zai duba abubuwan da suka shafi kama su, tsare su da sakin su."
"Dukkanin hukumomin tsaron da suke da alaƙa da lamarin za a bincike su kuma duk wanda aka samu da laifi zai fuskanci hukunci."
- Mohammed Idris
Jigon PDP ya caccaki tsare yara
A wani labarin kuma, kun ji cewa wani jigo a jam’iyyar PDP, Cif Olabode George, ya yi Allah-wadai da gurfanar da yaran da aka tsare saboda zanga-zanga a gaban kotu.
Gurfanar da yaran da aka yi a gaban kotu ya jawo mutane sun yi ta tofin Allah tsine tare da nuna ɓacin ransu kan hakan.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng