Matsafi Ya Kashe Mata 76 Ya Cinye Namansu, Ya Fadi Alaƙarsa da 'Yan Siyasa
- Rahotanni da suka fito daga jihar Oyo sun tabbatar da wani mutum ya yi ikirarin kashe mata kusan 100 yana shan jini da cin namansu
- Matsafin mutumin ya bayyana cewa yana amfani da jinin matan ne wajen tsafe tsafe sai kuma ya cinye namansu daga baya
- Ya kuma tabbatar da cewa yana da alaka da manyan masu kudi da shahararrun ma'aikata da yan siyasa da suke iya ba shi aiki
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Oyo - Wani mutum da ake kira da Mistina Orobo ya bayyana a jihar Oyo inda ya ba da labarin cewa ya kashe mata kusan 100.
Mistina Orobo ya bayyana cewa wuraren da suka fi dadin ci a jikin dan dama su ne harshe, tafin hannu da afin kafa.
Jaridar Punch ta wallafa cewa mutumin ya ce yana da alaka da manyan yan siyasa a lokacin da yake aikata laifin.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Matsafin ya kashe mata 76 a Oyo
Wani matsafi da aka fi sani da Mistina Orobo ya tabbatar da cewa ya kashe mata sama da 76 a rayuwarsa da ya yi a baya.
Mistina Orobo ya tabbatar da cewa yana kashe matan ne sai ya yi amfani da jininsu wajen tsafi daga baya kuma ya cinye namansu.
Sai dai a halin yanzu ya bayyana cewa ya tuba ya kuma shafe shekaru sama da hudu yana koyon ilimin zama kwararren fasto.
Matsafi ya fadi dalilin kashe mata 76
Rahoton Legit ya nuna cewa Mistina Orobo ya ce ya shafe shekaru bakwai yana kashe mata kuma yawanci yana samun wadanda yake kashewa ne a gidajen casu.
Ya kuma tabbatar da cewa yana amfani da jinin matan da namansu ne domin tsafi ta inda bindiga ko suka da wuka ba sa kama shi.
Matsafin ya yi ikirarin cewa yana da alaka da yan siyasa da manyan ma'aikata kuma ana ba shi kwangilar kashe mutane.
Dalilin tuban matsafin daya kashe mata 76
Matsafin mai suna Mistina Orobo ya ce an taba kashe shi amma wani gunki da yake da shi a gida ya dawo masa da ransa.
Bayan an dawo masa da rai sai ya fita daukar fansa amma da ya isa wajen sai aka ba shi hakuri daga nan kuma imani ya fara shiga zuciyarsa.
An kama matsafi a jihar Delta
A wani rahoton, kun ji cewa yan sandan jihar Delta sun kama wadanda ake zargi da garkuwa da mutane da dama tare da wasu matsafi a yankuna daban daban.
Ana zargin yan bindigar da aka kama da yawaita ayyukan ta'addanci a yankunan Warri, Ugheli, Sapele da sauran wurare a fadin jihar.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng