Mijina matsafi ne, yana son ya yi kudi dani - Wata mata ta roki kotu a raba aurenta

Mijina matsafi ne, yana son ya yi kudi dani - Wata mata ta roki kotu a raba aurenta

Wata mata mai yara hudu, Modupe Oyelade a ranar Laraba, ta shigar da kara wata kotun gargajiya a Ibadan inda ta nemi a rushe aurenta da mijinta, Aderemi na tsawon shekaru 17.

Hujjar ta na neman raba wannan aure shine cewa mijinta ya yi yunkurin yin kudi da ita.

Modupe, wacce ke zama a yankin Iyana-Church a Ibadan, ta fada ma shugaban kotun, Cif Ademola Odunade, cewa mijinta ya yi kokarin kashe ta domin ya azurta kansa.

“Ya yi mun karyar cewa ya je makaranta.

“Bai da takardar shaidar kammala karatu da ke nuna hakan.

“Bayan mijina ya hana kokarina na son ci gaba da karatuna a jami’a, sai na samu tallafi daga abokaina sannan na kammala karatu.

“Yana so ya ga ya tara dukiya cikin sauri kuma ni yake hari.

“Na kan yi zubar jini duk lokacin da na kwanta bacci tare da shi.

“Ina ganin kwaryar tsafi a kaina cikin mafarkina kuma a dakin baccina.

“Wasu lokutan idan muna a kan gado, mijina na wasu surkulle da tsakar dare wanda ke nuna mugun nufinsa a kaina.

“Da na ga wadannan alamu, sai na bar masa gidan, amma sai fasto dinmu ya shiga lamarin sai na koma gida.

“Na sake barin gidan, amma sai ya nemo ni tare da makasa wadanda suka tona masa asiri sannan suka gargade ni da na yi a hankali,” in ji ta.

Mijina matsafi ne, yana son ya yi kudi dani - Wata mata ta roki kotu a raba aurenta
Mijina matsafi ne, yana son ya yi kudi dani - Wata mata ta roki kotu a raba aurenta Hoto: Thisday
Asali: Twitter

Sai dai wanda ake karan ya yi adawa da lamarin sannan ya karyata zargin da ake masa.

Aderemi ya yi korafin cewa matarsa mazinaciya ce da ke bin maza.

KU KARANTA KUMA: An tube rawanin mai unguwar da ake zargi da sayar da yaro a Kano

“Ban yi kowani yunkuri na kudi da ita ba.

“Kuma na kasance mai dauke dawainiyar yaranmu,” in ji Aderemi.

Da yake zartar da hukunci, Odunade ya raba auren inda ya nuna barazana ga rayuwa a matsayin hujjar kotu na yanke wannan hukunci.

Ya mika ragamar kula da yaran hudu ga mahaifiyarsu sannan ya umurci wanda ake kara da ya dunga biyan an20,000 duk wata a matsayin kudin abincinsu sannan shi zai dauki dawainiyar karatunsu da sauran harkokinsu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel