Tsadar Rayuwa: Tinubu Ya Fadi Abin da Ya Sani kan Halin da 'Yan Najeriya Suke Ciki
- Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya taɓo batun tsadar rayuwa da ƴan Najeriya suke fama da shi a halin yanzu
- Bola Tinubu ya bayyana cewa tabbas rayuwa ta yi tsada amma ana ɗaukar matakan ganin abubuwa sun gyaru
- Sannan ya yi nuni da cewa matsalar tattalin arziƙin da ake fama da ita, abu ne wanda ya zama ruwan dare a ƙasashen duniya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya yi magana kan tsadar rayuwar da ake fama da ita a ƙasar nan.
Shugaba Tinubu ya amince cewa akwai tsadar rayuwa a ƙasar nan, inda ya tabbatarwa ƴan Najeriya cewa gwamnatinsa na ɗaukar matakai na rage wahalhalu da farfaɗo da tattalin arziƙin ƙasar nan.
Shugaba Tinubu ya bayyana haka ne a ranar Litinin a jawabinsa bayan rantsar da sababbin ministoci bakwai a fadar shugaban ƙasa da ke Abuja, cewar rahoton jaridar Leadership.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Bola Tinubu ya magantu kan tsadar rayuwa
Shugaba Tinubu ya bayyana cewa ƙalubalen da ake fuskanta ba a Najeriya ba ne kaɗai, har ma da sauran ƙasashen duniya.
Shugaban ya bayyana ƙoƙarin da Najeriya ke yi kan matsalar ƙalubalen tattalin arziƙin duniya wanda ya shafi ƙasashen duniya ciki har da na Turai da Amurka.
"Tabbas, rayuwa ta yi tsada. Na yarda da hakan. Mun sauke nauyin biyan sabon mafi ƙarancin albashi ga dukkanin ma'aikata."
"Mun samu kanmu cikin matsala. Sauran ƙasashe ma haka, a kusa da mu da nesa da mu suna fuskantar ƙalubale. Annobar Korona ta gigita tattalin arziƙin duniya, amma muna ci gaba da aiki tuƙuru."
- Shugaba Bola Tinubu
Tinubu ya yabawa ministoci
Da yake jawabi ga sababbin ministocin da aka rantsar, shugaba Tinubu ya yaba da yadda suke son hidimtawa ƙasar nan a wannan lokacin mai wahala.
"Ba abu ba ne mai sauƙi a samu mutanen da za su ba da rayukansu, ƴancinsu, da kuma nauyin da ya rataya a wuyansu domin yi wa ƙasarsu hidima, musamman a wannan lokacin mai cike da ƙalubale."
- Shugaba Bola Tinubu
Tinubu na ƙoƙarin rage raɗadi
A wani labarin kuma, kun ji cewa ministan yada labarai da wayar da kan jama’a, Mohammed Idris, ya yi magana kan tsadar rayuwa a gwamnatin shugaba Bola Tinubu.
Ministan ya nanata ƙudirin Shugaba Tinubu na rage raɗaɗin tattalin arziƙin da ƴan Najeriya ke fuskanta, musamman saboda cire tallafin man fetur.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng