Yan Bindiga Sun Yi Ta'asa, An Harbe Ɗan Gwagwarmaya a gaban Iyalansa a Katsina
- Wasu miyagun yan bindiga sun kai hari garin Mai Turare da ke karamar hukumar Dutsinma a jihar Katsina
- Mutanen dauke da miyagun makamai sun farmaki gidan wani sanannen dan fafutuka, Ibrahim Mai Kaita
- An san Ibrahim Mai Kaita da bayyana ra'ayinsa kan abubuwan da za su kawo ci gaba yankin Arewacin Najeriya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Katsina - Yan bindiga sun tafka danyen aiki bayan sun kai mummunan hari gidan wani mai fafutuka a jihar Katsina.
Yan bindigar sun kutsa gidan matashin dan fafutuka, Ibrahim Mai Kaita a gidansa da ke garin mai Turare a karamar hukumar, Dutsin-ma da ke Katsina.
TVC Television ta wallafa cewa yan ta'addan sun sace matan Ibrahim Mai Kaita guda biyu zuwa wani wuri da har yanzu ba a kai ga sanin ina ne ba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yan bindiga sun harbi dan fafutuka
Jaridar Daily Post ta wallafa cewa yan bindiga sun je har gida tare da harbe mai fafutuka, Ibrahim Mai Kaita har lahira.
Ibrahim Mai Kaita sananne ne wajen furta ra'ayinsa a kan ayyukan gwamnatin Katsina da fafutukar samun ci gaba a shiyyar Arewacin Najeriya.
Yan bindiga sun matsa da kai hare hare
Harin da yan bindiga ke kai wa sassan jihar Katsina inda a baya-bayan nan su ka farmaki mazauna unguwar Mai Turare da ke karamar hukumar Dutsin -ma a Katsina.
Wannan na zuwa duk da gwamnatin Umaru Dikko Radda ta bayyana jajircewarta wajen hada kan jami'an tsaron sa kai wajen dakile ta'addanci a jihar Katsina.
Katsina: Gwamna ya koka kan karuwar ta'addanci
A baya mun ruwaito cewa gwamnan jihar Kaduna, Uba Sani ya bayyana takaicin yadda ake samun kyankyashe yan ta'adda a jami'o'in kasar nan har ya buga misali da Katsina.
Gwamna Uba Sani ya yi takaicin yadda manyan makarantu da ake zaton za su samar da mutane na gari su ke kyankyashe bara gurbi, kamar yadda aka kama alburusai a jami'ar Dutsin-Ma da ke Katsina.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng