Shugaba Tinubu Ya Rantsar da Sababbin Ministoci 7 a Abuja, Bayanai Sun Fito
- Bola Ahmed Tinubu ya rantsar da sababbin ministoci bakwai a fadar shugaban ƙasa da ke Abuja ranar Litinin, 4 ga watan Nuwamba, 2024
- Shugaban kasa Tinubu ya shaidawa ministocin cewa ya naɗa su, su shiga tawagarsa don bada gudummuwa wajen ceto Najeriya
- Wannan dai na zuwa ne bayan majalisar dattawan Najeriya ta tantance tare da amincewa da naɗin sababbin ministocin a makon jiya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
State House, Abuja - Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya rantsar da sababbin ministoci bakwai da ya nada a Aso Villa da ke birnin tarayya Abuja.
Wannan dai na zuwa ne bayan majalisar dattawa ta tantance tare da amincewa da naɗin ministocin a makon da ya gabata.
Channels tv ta tattaro cewa Tinubu ya naɗa sababbin ministocin ne a lokacin da ya yi garambawul a gwamnatinsa, ya sallami mutum 6 daga aiki.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ministoci 7 da suka kama aiki yau
Sababbin ministocin da aka rantsar sun haɗa da Nentawe Yilwatda a matsayin ministan jin ƙai da rage talauci da Muhammadu Maigari Dingyadi a matsayin ministan kwadago.
Sai kuma Bianca Odinaka Odumegwu-Ojukwu, ƙaramar ministar harkokin ƙasahen ketare, Jumoke Oduwole, ministan masana'antu, kasuwanci da zuba jari da Idi Mukhtar Maiha, ministan harkokin kiwon dabbobi.
Sauran su ne, Yusuf Abdullahi Ata, ƙsramin ministan gidaje da raya birane, da Suwaiba Said Ahmad a matsayin ƙaramar Ministar ilimi.
Shugaba Tinubu ya buƙaci su sauke nauyi
Da yake jawabi ga ministocin, Shugaba Tinubu buƙaci su yi kokarin sauke nauyin da ya ɗora masu domin ɗaga Najeriya zuwa matakin ci gaba.
"Najeriya tana saman ruwa kuma jirginta ba zai nutse ba, duk wuya duk runtsi ba zamu gujewa nauyin da aka ɗora mana ba.
"Ina alfaharin zama jagoranku kuma na shirya shigewa gaba domin ku samu nasara, mun tauna tsakuwa don aya ta shiga taitayinta.
- Bola Tinubu.
Shugaba Tinubu ya faɗawa sababbin ministocin cewa ya naɗa su ne don su ba ɗa gudummuwarsu wajen ceto Najeriya, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.
Tinubu ya umarci ministoci su rage kashe kudi
A wani labarin, an ji cewa Bola Tinubu ya umarci ministoci da shugabannin hukumomin gwamnatin tarayya su rage motocin da ke cikin ayarinsu.
Shugaban kasar ya kuma umarci ministoci da shugabannin hukumomin su rage yawan jami'an tsaronsu zuwa jami'ai biyar.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng