Dillalan Mai 4 Sun Shigo da Fetur na N833bn yayin da Dangote Ya Fadi Farashinsa

Dillalan Mai 4 Sun Shigo da Fetur na N833bn yayin da Dangote Ya Fadi Farashinsa

  • Fitattun ‘yan kasuwar mai hudu sun kashe kimanin Naira biliyan 833 wajen shigo da mai a cikin watanni tara na shekarar 2024
  • Manyan dillalan da suka shigo da man sun hada da TotalEnergies Marketing Nigeria, MRS Oil Nigeria, Eterna Plc da Conoil Plc
  • Rahoton ya dogara ne akan bayanan kuɗin kamfanonin na watanni tara, wanda aka wallafa a kamfanin hada-hadar kudi (NGX)

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Wasu fitattaun ‘yan kasuwar mai a Najeriya sun ci gajiyar janye tallafin da kasar ke bayarwa kan kayayyakin man fetur.

Janye tallafin man ya ba dillalan damar yin kasuwanci a cikin yanayin da kasuwa ke kayyade farashi, wanda hakan ke haifar da karuwar ribar da suke samu.

Kara karanta wannan

Ba a gama da Kano ba, gwamnatin Zulum ta gurfanar da kananan yara da wasu 16

Manyan 'yan kasuwa sun samu riba mai yawa yayin shigo da man fetur
Manyan 'yan kasuwar mai sun baje kolin ribar da suka samu daga sayar da man fetur. Hoto: Bloomberg/Contributor
Asali: Getty Images

'Yan kasuwa 4 sun samu ribar N465.92bn

Wani rahoto na kamfanin hada hadar kudin Najeriya (NGX) ya nuna cewa wasu fitattun ‘yan kasuwa hudu sun samu kusan Naira tiriliyan 1.3 inji Punch.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Duk da makudan kudin da ake kashewa wajen shigo da mai, kamfanonin hudu sun kashe Naira biliyan 833.86 wajen shigo da albarkatun man a cikin wannan lokaci.

Sai dai kuma shigo da man na Naira biliyan 833.86 ya kara yawan ribar da suke samu zuwa Naira biliyan 465.92 daga Janairu zuwa Satumbar 2024.

Janye tallafi ya taimakawa 'yan kasuwa

Businessday NG ya rahoto cewa kamfanonin man hudu sun hada da TotalEnergies Marketing Nigeria, MRS Oil Nigeria, Eterna Plc da Conoil Plc.

Sakamakon cire tallafin man fetur, 'yan kasuwar sun shawo kan hauhawar farashin aiki tare da samun habakar arzikinsu da kashi 100 a cikin watanni taran.

Kara karanta wannan

Matsala ta kunno kai a Kano, takardun Naira sun fara ƙaranci a hannun jama'a

A watan Mayun 2023, Shugaba Bola Tinubu ya sanar da cire tallafin man fetur, wanda ya haifar da tashin farashin man daga N200 a Mayun bara zuwa N1060 a watan Nuwamba 2024.

Dangote ya fadi farashin feturinsa

Tun da fari, mun ruwaito cewa matatar man Dangote ta sanar da cewa tana siyar da man fetur kan N960 ga jiragen ruwa da kuma N990 ga manyan motoci.

Matatar Dangote ta bayyana cewa farashin da take sayar da man fetur ɗinta ya fi arha fiye da duk wani man da aka shigo da shi daga ƙasashen waje.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.