Aso Villa Ta Dauki Harama, An Fara Shirin Rantsar da Ministoci
- A safiyar yau Litinin shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu zai rantsar da sababbin ministoci da ya naɗa domin fara aiki
- Rahotonni na nuni da cewa a yanzu haka an fara taro a fadar shugaban kasa inda wasu ministocin suka fara isa dakin taro
- A makon da ya wuce ne majalisar dattawan Najeriya ta kammala tantance dukkan ministoci bakwai da Bola Ahmed ya naɗa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Rahotanni na nuni da cewa yan uwa da abokan arziki sun isa fadar shugaban kasa domin rantsar da ministoci.
Dama dai a yau Litinin ne fadar shugaban kasa ta bayyana cewa za a rantsar da sababbin ministocin da Bola Tinubu ya naɗa.
Rahoton Channels Television ya nuna cewa a yanzu haka ana jiran isowar wasu daga cikin jami'an gwamnati domin rantsar da ministocin.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An fara shirin rantsar da ministoci
Rahotanni na nuni da cewa sababbin ministoci da shugaban kasa Bola Tinubu ya nada sun isa Aso Villa domin rantsar da su.
Haka zalika an ruwaito cewa sababbin ministocin sun isa fadar shugaban kasa ne tare da yan uwa da abokan arziki domin shaida taron rantsuwar.
A makon da ya wuce ne majalisar dattawan Najeriya ta kammala tantance dukkan mutane bakwai da Bola Tinubu ya tura mata a matsayin ministoci.
Dakin taro bai gama cika ba har yanzu
Sai dai duk da cewa dukkan sababbin ministocin sun hallara, an ruwaito cewa dakin taron bai kammala cika ba.
A yanzu haka dai ana jiran isowar wasu ministoci da sauran manyan jami'an gwamnati kafin taron ya kankama.
Shugaban kasa Bola Tinubu ya kori ministoci biyar a watan da ya wuce kuma ya kara daukar bakwai a kokarin gyara tafiyar mulkinsa.
Tinubu ya yi martani ga Atiku
A wani rahoton, mun ruwaito muku cewa gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ta yi martani ga kalaman tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar bisa tsare-tsarenta
Hadimin shugaban kasa kan harkokin yada labarai da dabaru, Bayo Onanuga ne ya yi magana a sanarwar da ya fitar a daren Lahadi.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng