Gwamna Zai Dakile Matsalar Lantarki, An Hada Kai da Kamfanin China

Gwamna Zai Dakile Matsalar Lantarki, An Hada Kai da Kamfanin China

  • Gwamnatin Gombe ta dauko aikin da zai kawo karshen matsalar wutar lantarki a jihar bayan Arewa ta fuskanci irin matsalar
  • Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya zai yi aiki da kamfanin China domin samar da tashar lantarki mai amfani da hasken rana
  • Gwamnatin Gombe ta rattaba hannu a kan yarjejeniyar gina tashar lantarki mai amfani da hasken rana mai girman megawat 100

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Gombe - Gwamnatin Gombe ta rattaba hannu da kamfanin China 18th Engineering domin kawo karshen matsalar hasken lantarki a jihar.

Yarjejeniyar ta kunshi gina tashar wutar lantarki mai amfani da hasken rana mai girman megawatt 100 a Gombe domin a wadata jama'ar jihar da haske.

Kara karanta wannan

Band A: Masu samun wutar awa 20 a rana sun gaji, sun kai kuka wajen Tinubu

Gwamna
Gwamnatin Gombe za ta samar da magance matsalar lantarki Hoto: Ismaila Uba Misilli
Asali: Facebook

Jaridar Daily Trust ta wallafa cewa darakta janar kan yada labaran gwamnan Gombe, Ismaila Uba Misilli ya sanar da sabon tsarin da gwamnatin jihar ta bijiro da shi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Za a gina tashar wutar lantarki a Gombe

Voice of Nigeria ta tattaro cewa gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya ya zauna da jagororin kamfanin 'China Railway 18th Bureau' don gina tashar lantarki a Gombe.

Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya ya bayyana cewa wannan na daga cikin shirin gwamnatinsa na ganin Gombe ta tsaya da kafarta a fannin samar da wutar lantarki.

Gwamnatin Gombe ta dauko aikin lantarki

Gwamnatin Muhammadu Inuwa ta ce aikin kawo tashar wutar lantarki mai amfani da hasken rana zai samarwa da matasan jihar Gombe aikin yi.

A jawabinsa a madadin gwamnan, kwamishinan makamashi da albarkatun kasa, Sanusi Ahmad Pindiga ya ce irin wannan tasha za ta magance irin matsalar lantarki da aka samu a kasar nan.

Kara karanta wannan

Rashin lantarki: An fara haɗa alkaluman asarar Arewa, za a nemi diyya daga Tinubu

Gwamnati za ta magance matsalar lantarki

A baya mun ruwaito cewa gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ta bayyana mafita domin magance afkuwar irin matsalar lantarkin da aka fuskanta a Arewacin kasar nan.

A ziyarar da ya kawo jihar Kano, Ministan makamashi, Adebayo Adelabu ya ce gwamnatin Bola Ahmed Tinubu za ta samar da tashoshin lantarki a jihohi domin magance matsalar.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.