Gwamna Ya Shirya Rage Masu Zaman Kashe Wando, Zai Dauki Mutum 10,000 Aiki

Gwamna Ya Shirya Rage Masu Zaman Kashe Wando, Zai Dauki Mutum 10,000 Aiki

  • Gwamnatin jihar Bauchi ta sanar da shirin da take da shi domin rage mutanen da suke zaune babu aikin yi
  • Gwamna Bala Mohammed ya bayyana cewa gwamnatinsa ta shirya ɗaukar mutum 10,000 aiki a jihar
  • An ware kuɗaɗe domin siyan amfanin gona wanda daga baya za a siyar da shi ga jama'a kan farashi mai rahusa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Bauchi - Gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed ya bayyana shirin gwamnatinsa na ɗaukar ma’aikata aiki.

Gwamna Bala ya bayyana cewa gwamnatinsa na shirin ɗaukar ma'aikata 10,000 aiki zuwa ƙarshen shekarar 2024.

Gwamnan Bauchi zai dauki aiki
Gwamna Bala Mohammed zai dauki aiki a Bauchi Hoto: Senator Bala Abdulkadir Mohammed
Asali: Twitter

Gwamnan Bauchi na sane da ƙarancin ma'aikata

Gwamna Mohammed ya ce gwamnati na sane da rashin isassun malamai a makarantu, ma’aikatan jinya a asibitoci da kuma ƙarancin ƙwararru a fannin noma, cewar rahoton jaridar Leadership.

Kara karanta wannan

APC ta mayar da martani ga gwamna kan shirinsa na neman kujerar Tinubu a 2027

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamnan ya ba da tabbacin cewa zai yi abin da ya dace domin cike giɓin da ake da shi a waɗannan fannonin.

Gwamna Bala ya bayyana haka ne a wurin taron tunawa da cikarsa shekara 66 a Bauchi a ranar Lahadi.

Gwamnati za ta tallafawa jama'a a Bauchi

Ya nanata cewa gwamnatin jihar Bauchi ta ware Naira biliyan uku domin siyan kayan abincin da aka girbe domin siyarwa jama’a a kan farashi mai rahusa.

Gwamna Bala Mohammad ya ci gaba da cewa, za a ƙara daukar ƙarin ma’aikatan aikin gona domin bunƙasa kuɗin shiga da manoma ke samu da kuma tabbatar da samar da abinci a jihar Bauchi.

Ya bayyana cewa, an shirya horar da matasa 10,000 a fannin ICT domin su zama masu dogaro da kansu.

Gwamnatin Bauchi ta kai buƙata gaban majalisa

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun sake kai mummunan hari, sun kashe uba da yaƴansa 2

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnatin Bauchi ƙarƙashin jagorancin Gwamna Bala Mohammed ta miƙa sabuwar buƙata a gaban majalisar dokokin jihar.

Gwamnatin ƙarƙashin jagorancin Gwamna Bala Mohammed ta gabatar da ƙarin kasafin kuɗi na Naira biliyan 94.676 ga majalisar dokokin jihar domin neman amincewa da shi.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng