FUDMA: Yadda Aka Karrama Matar Tinubu, Akpabio a Arewacin Najeriya

FUDMA: Yadda Aka Karrama Matar Tinubu, Akpabio a Arewacin Najeriya

  • Jami'ar tarayya da ke Dustin-ma a jihar Katsina ta girmama wasu jiga jigan yan siyasa da digirin digirgir saboda cigaba da suke kawowa
  • Shugaban majalisar dattawa, Sanata Godswill Akpabio da matar shugaban kasa, Oluremi Bola Tinubu na cikin waɗanda aka girmama
  • Godswill Akpabio ya nuna godiya bisa karrama shi da aka yi da digirin girmamawar da kuma zakulo shi da aka yi cikin miliyoyi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Katsina - Jami'ar tarayya da ke Dutsin-ma ta karrama manyan yan siyasa wajen ba su digirin digirgir na girmamawa.

Shugaban majalisar dattawa, Sanata Godswill Akpabio ya kasance cikin wadanda jami'ar ta girmama.

Akpabio
FUDMA ta girmama Akpabio da wasu yan siyasa. Hoto: Nigerian Senate
Asali: Facebook

Jaridar Daily Trust ta wallafa cewa matar shugaban kasa, Sanata Oluremi Bola Tinubu na cikin waɗanda aka girmama a jami'ar.

Kara karanta wannan

Gwamnati ta yi martani ga Atiku, ta fadi abin da zai faru idan da PDP ke mulki

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An karrama matar Tinubu da Akpabio

Jami'ar tarayya da ke Dutsin-ma ta girmama shugaban majalisar dattawa, Sanata Godswill Akpabio da digirin digirgir.

Haka zalika matar shugaban kasa, Oluremi Tinubu da Sanata Aliyu Magatakarda Wammako na cikin waɗanda aka girmama a jami'ar.

Jaridar This Day ta wallafa cewa dan majalisar wakilai mai wakiltar Bichi, Abubakar Kabir Abubakar na cikin waɗanda jami'ar ta girmama da digirin digirgir.

Akpabio ya yi godiya ga jami'ar FUDMA

Sanata Muntari Dandutse da ya wakilci Godswill Akpabio ya ce shugaban majalisar ya mika godiya ga jami'ar FUDMA bisa girmama shi da ta yi.

Muntari Dandutse ya kara da cewa girmama Sanata Akpabio ya shafi dukkan iyalansa da abokansa a harkar siyasa.

A ƙarshe Sanata Dandutse ya kara da cewa suna farin ciki kan yadda makarantu suke girmama su lura da gudunmawar da suke ba al'umma.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu ya yi ƙus ƙus da sanatocin PDP 3 a Abuja, bayanai sun fito

Yar Tinubu ta zama jakadar almajirai

A wani rahoton, kun ji cewa a'aikatar lura da almajirai da yaran da ba su zuwa makaranta ta ba yar Bola Ahmed Tinubu matsayin jakadarta.

Shugaban ma'aikatar almajirai, Muhammad Sani Idris ne ya bayyana lamarin a wata ziyara da ya kai wa yar shugaban kasar a Legas.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng