Lauya Ya Bayyana Yadda aka Ci Mutuncin Arewa kan Yaran Zanga Zanga
- Lauya mai kare yaran da aka kama a lokacin zanga zangar tsadar rayuwa, Hamza Nuhu Dantani ya yi karin haske kan halin da ake ciki
- Barista Nuhu Hamza Dantani ya yi zargin cewa ba a bi ƙa'ida wajen kama yaran ba kuma an karya doka wajen gabatar da su a kotu
- Lauyan ya bayyana hanyoyin da manyan yan siyasa da Malamai a Arewa za su bi wajen ganin an fito da su ba tare da bata lokaci ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Lauya mai kare yaran da aka kama a lokacin zanga zangar adawa da tsadar rayuwa ya yi bayani kan yadda za a fitar da su daga kurkuku.
Barista Nuhu Hamza Dantani ya bayyana cewa an azabtar da yaran da yunwa har sai da suka gigice.
DCL Hausa ta wallafa bidiyon hirar da ta yi da Barista Nuhu Hamza Dantani a shafinta na Facebook.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Halin yunwa da yaran suka shiga
Barista Nuhu Hamza Dantani ya bayyana cewa an tsare yaran tsawon watanni uku ba tare da suna samun abinci wadatacce ba ko gurfanar da su.
Lauyan ya kara da cewa yaran sun gigice saboda yunwa ta inda suke gagara gane ina hankalinsu yake.
A cewar lauyan, abin da aka musu ya saba doka kuma cin mutunci ne ga Arewacin Najeriya domin lamarin ya shafi yankin.
Bin ka'ida wajen kama yaran zanga zanga
Barista Nuhu Hamza Dantani ya ce da an bi ƙa'ida wajen kama yaran da za a sallami da dama daga cikinsu tun a Kano.
Lauyan ya bayyana cewa akwai yaron da aka kama ya fito sayen magani ga yar uwarsa da ba ta da lafiya a cikin wadanda aka gurfanar.
Yadda za a fitar da yaran zanga zanga
Lauya mai kare yaran zanga zanga ya ce ya kamata malamai da suka tallata Bola Tinubu su saka baki a cikin lamarin.
Haka zalika ya kara da cewa dole yan siyasar Arewa su saka baki duk da cewa suna jin tsoron shiga lamarin domin gudun bacin suna.
Amnesty ta bukaci sakin yan zanga zanga
A wani rahoton, kun ji cewa kungiyar Amnesty International ta bukaci gwamnatin Najeriya ta saki yaran da aka kama a lokacin zanga zanga.
Amnesty International ta ce kama yara ƙanana ya saba dokar kasa kuma abin kunya ne ga gwamnatin Najeriya ta gurfanar da yaran a gaban kotu.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng