"Na Mu Ya fi Arha": Matatar Dangote Ta Fadi Farashin da Take Siyar da Fetur

"Na Mu Ya fi Arha": Matatar Dangote Ta Fadi Farashin da Take Siyar da Fetur

  • Matatar Dangote ta fito ta bayyana farashin da take siyar da man fetur ɗin da ta tace ga ƴan kasuwa
  • Dangote ya bayyana cewa farashin da yake siyar da fetur ya fi arha fiye da wanda ake shigowa da shi daga ƙasashen waje
  • Ta musanta iƙirarin da wasu ƴan kasuwa suka yi na cewa yafi sauki a shigo da fetur daga waje kan siya a matatar saboda tsada

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Legas - Matatar Dangote ta bayyana farashin man fetur ɗin da take tacewa inda ta ce na ta ya fi arha fiye da wanda aka shigo da shi daga ƙasashen waje.

Matatar man Dangote ta bayyana hakan ne a matsayin martani ga wasu ƴan kasuwa da suka yi iƙirarin cewa shigo da fetur ya fi arha fiye da wanda ake samowa daga matatar Dangote.

Kara karanta wannan

SERAP ta ba Tinubu wa'adi kan yaran da aka tsare, ta fadi matakin dauka

Matatar Dangote ta fadi farashin fetur
Matatar Dangote ta ce farashin fetur dinta na da arha Hoto: Bloomberg
Asali: Getty Images

Martanin na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa daga jami'in sadarwa na gamayyar kamfanonin Dangote, Anthony Chiejina, wacce ya sanya a shafin X.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya bayyana ikirarin da IPMAN da sauran ƴan kasuwa suka yi a matsayin abin da ba haka yake ba.

Menene farashin fetur ɗin Dangote?

Sanarwar ta bayyana cewa matatar ta fara siyar da fetur a kan Naira 960 kan kowacce lita domin siyarwa ga masu jiragen ruwa yayin da take sayarwa masu siya da manyan motoci a kan farashin N990.

Ya yi bayanin cewa matatar ta sanya farashinta ƙasa da farashin kasuwannin duniya.

"Idan wani ya yi iƙirarin zai iya shigo da fetur a farashi mafi arha kan yadda muke siyarwa, to suna shigo da gurɓatacce ne tare da haɗa baki da ƴan kasuwan ƙasashen waje domin kawo mai ƙaramin inganci."

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun sake kai mummunan hari, sun kashe uba da yaƴansa 2

"Ba tare da yin la'akari da lafiyar ƴan Najeriya ko kuma ƙarkon ababen hawansu ba."

- Anthony Chiejina

Dalilin kasa jigilar fetur daga matatar Dangote

A wani labarin kuma, kun ji cewa ƙungiyar dillalan man fetur ta IPMAN, ta yi magana kan dalilin kasa fara jigilar fetur daga matatar Dangote.

Ƙungiyar IPMAN ta bayyana cewa har yanzu suna kan tattaunawa da matatar Dangote kan sharuɗan fara jigilar man.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng