Meye Gaskiyar Cewa Dangote Ya Daga Farashin Man Fetur da Yake Tacewa a Najeriya?
- Matatar man Dangote ta ce ba gaskiya bane cewa farashin man fetur da take tacewa ya zarce na waje a tsada
- An zargi kamfanin Dangote da yiwa ‘yan Najeriya tsadar mai duk da tace shi a nan gida duba da wasu dalilai
- Dillalan man fetur sun magantu kan farashin mai a kamfanin Dagote da kuma yadda yake a daga kasashen waje
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Legas, Najeriya - Matatar Dangote ta yi watsi da zargin sayar da man fetur farashi tsakanin N1, 015 zuwa N1, 028/lita.
Dillalan man fetur sun yi batun cewa, man da matatar Dangote ta tace ya kai N1,015 zuwa N1,028 a kowanne lita, inda suka ce man da ake shigo dashi daga waje a watan Oktoba ya zo ne a N978.01.
Da yake martani ga wannan ikrarin, jami’in sadarwa na gamayyar kamfanonin Dangote, Tony Chiejina ya ce batun dillalan ba komai bane face karya, rahoton Vanguard.
Abin da dillalan man fetur ke cewa
A cewar wasu bayanai da suka fito daga ofishin kungiyar dillalan makamashi na Najeriya a ranar Alhamis, kudin dizel ya kai N1,069.97 kowanne lita yayin da man jirgin sama kuma ya kai akalla N1,119.67 a lita.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wani babban dillalin mai da ya nemi a sakaya sunansa ya ce, matatar tana siyarwa manyan diloli litar man fetur a kan kudi N1,015 yayin da kananan dillalai ke saye a kan N1,028.
A cewarsa:
“Dangote na sayar da mai ga manyan diloli a kudin N1,015 a lita, amma ga kananan diloli da ke sayen kadan-kadan, ana sayar musu a N1,028 kan kowanne lita.”
Sai dai, sakataren yada labarai na kuntiyar dillalan mai ta PETROAN, Dr Joseph Obele ya ce, farashin man Dangote ka iya tsada ne duba da yadda kamfanin ke tace man da ya sayo a kasashen waje.
Yadda man Dangote ya fi kowanne tsada
A baya kadan, kungiyar dillalan mai masu zaman kansu IPMAN ta bayyana cewa farashin man feturin matatar Dangote ya fi tsada fiye da sauran wuraren da ake sayo mai.
IPMAN ta ce wannan ya sa 'ya'yanta suke gujewa sayen man feturin Dangote, su saya daga wasu manyan wuraren kasuwancin fetur a fadin kasar nan.
Mataimakin sakataren IPMAN na kasa, Yakubu Suleiman ne ya fadi haka da yake jawabi a cikin shirin safe na gidan talabijin na Arise ranar Juma'a.
Asali: Legit.ng