Shugaba Tinubu Ya Shirya Rantsar da Sababbin Ministoci, Ya Sanya Lokaci

Shugaba Tinubu Ya Shirya Rantsar da Sababbin Ministoci, Ya Sanya Lokaci

  • Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya shirya rantsar da sababbin ministoci guda bakwai da ya naɗa a gwamnatinsa
  • Shugaba Tinubu zai rantsar da sababbin ministocin a ranar Litinin, 4 ga watan Nuwamba a zauren majalisar zartaswa da ke fadar shugaban ƙasa
  • Rantsarwar da Tinubu zai yi musu na zuwa ne bayan majalisar dattawa ta tantance su tare da amincewa da naɗin da aka yi musu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Fadar shugaban ƙasa ta bayyana lokacin da Shugaba Bola Tinubu zai rantsar da sababbin ministocin da ya naɗa.

Shugaba Tinubu zai rantsar da sababbin ministocin a ranar Litinin 4 ga watan Nuwamba, 2024 a zauren majalisar zartaswa da ke Abuja.

Kara karanta wannan

Tinubu ya fadi lokacin kawo karshen matsalar rashin tsaro a Arewacin Najeriya

Tinubu zai rantsar da sababbin ministoci
Shugaba Tinubu zai rantsar da sababbin ministoci a ranar Litinin Hoto: Dr Jumoke Oduwole, Muhammad Maigari Dingyadi, Dr Nentawe Yilwatda Goshwe
Asali: Facebook

Mai ba shugaban ƙasa shawara na musamman kan yaɗa labarai da dabaru, Bayo Onanuga, ya bayyana hakan a ranar Lahadi a shafinsa na X.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tinubu zai rantsar da ministoci

"Shugaba Bola Tinubu zai rantsar da sababbin ministoci bakwai a gobe Litinin."
"Minitocin su ne Dr Nentawe Yilwatda, ministan jinƙai da rage talauci, Muhammadu Maigari Dingyadi, ministan ƙwadago da samar da aikin yi, Bianca Odumegwu-Ojukwu, ƙaramar ministan harkokin waje.
Sauran sun haɗa da Dr Jumoke Oduwole, ministar masana’antu, ciniki da zuba jari, Idi Maiha, ministan kiwon dabbobi, Yusuf Ata, ƙaramin ministan gidaje da raya birane da Dr Suwaiba Ahmad, ƙaramar ministar ilimi.
"Majalisar dattawa ta tantance ministocin a makon da ya gabata."

- Bayo Onanuga

Tinubu ya yi garambawul a gwamnatinsa

A wani garambawul da Tinubu ya yi wa majalisar ministocinsa a ranar 23 ga watan Oktoba, ya amince da sauyawa ministoci 10 ma'aikatu, ya sallami wasu biyar tare da naɗa sababbin ministoci bakwai.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu ya yi ƙus ƙus da sanatocin PDP 3 a Abuja, bayanai sun fito

A ranar 31 ga watan Oktoba, 2024, majalisar dattijawa ta tabbatar da sababbin ministocin guda bakwai bayan tantance kowanne daga cikinsu.

Majalisa ta amince da sababbin ministoci

A wani labarin kuma kun ji cewa majalisar dattawa ta amince da sababbin ministoci bakwai da shugaba Bola Tinubu ya naɗa bayan ya yi garambawul a gwamnatinsa.

Majiyar dattawan ta amince da ministocin ne bayan ta tantance su a ranar Laraba, 30 ga watan Oktoban 2024.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng