JAMB: Dubun 'Farfesa' Ya Cika, An Garkame Shi kan Yunkurin Rubutawa Yarsa Jarabawa

JAMB: Dubun 'Farfesa' Ya Cika, An Garkame Shi kan Yunkurin Rubutawa Yarsa Jarabawa

  • A shekarar 2019 hukumar jarabawa ta JAMB ta cafke wani Farfesa kan yunkurin rubuta wa yarsa jarabawa a birnin Tarayya da ke Abuja
  • A yau Lahadi 3 ga watan Nuwambar 2024 kotun majistare a Abuja ta daure Farfesa Jide Josiah Jisos har tsawon watanni shida
  • Hukumar JAMB ta tabbatar da cewa Farfesan ya yaudare su da cewa an turo shi ne ya duba yadda jarabawar ke tafiya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Kotun majistare a Abuja ta daure wani Farfesa a gidan kaso kan rubuta jarabawar UTME.

Kotun ta daure Farfesa Jide Josiah har watanni shida kan zargin kokarin rubuta wa yarsa jarabawa wanda ya saba ka'idar dokokin hukumar.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Tinubu ta fara shirin janye zarge zarge kan yara 32 a gaban kotu

An daure Farfesa kan yunkurin rubutawa yarsa jarabawar UTME
Kotu ta daure Farfesa watanni 6 a gidan kaso kan zargin rubutawa yarsa jarabawa. Hoto: Federal High Court.
Asali: Getty Images

JAMB: An kama Farfesa kan cin amanar jarabawa

Vanguard ta ruwaito cewa an cafke Farfesan ne a birnin Abuja a 2019 a makarantar Brix inda yar tasa ke shirin rubuta jarabawar a wannan shekara.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mai magana da yawun hukumar JAMB, Fabian Benjamin ya ce Farfesan ya yaudare su cewa shi jami'i ne da ke kula da jarabawar.

Ya ce ya zo ne daga kungiyoyin da ba na gwamnati ba domin tabbatar da yadda jarabawar ke tafiya domin ba da bahasi.

Yadda kotu ta daure Farfesa kan jarabawar UTME

Alƙalin kotun, Folashade Oyekan shi ya yanke hukuncin a kotun da ke Wuce Zone 2 a birnin Abuja, cewar Arise TV.

Oyekan ya ce an samu Farfesan da laifi guda daya kan zargin yunkurin rubutawa yarsa jarabawa inda aka daure shi watanni shida ko zabin biyan tara N100,000.

Kara karanta wannan

Hukumar gidajen yari ta yi magana kan zargin tsare yara 72, ta fayyace gaskiya

JAMB: Jami'o'in da suka laifi a Najeriya

A baya, kun ji cewa Hukumar JAMB ta koka kan yadda wasu jami'o'i a Najeriya ke ci gaba da bayar da gurbin karatu ba bisa ƙa'ida ba.

Shugaban JAMB na ƙasa, Farfesa Ishaq Oloyede ya bayyana sunayen wasu jami'o'i biyar da ake zargi da bada haramtaccen gurbi.

Oloyede ya ce gwamnatin tarayya ta yafewa kusan mutum miliyan ɗaya da aka gano sun samu gurbin karatu ba bisa ƙa'ida ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.