SERAP Ta ba Tinubu Wa'adi kan Yaran da Aka Tsare, Ta Fadi Matakin Dauka
- Ƙungiyar SERAP ta buƙaci shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya gaggauta umartar a saki yaran da aka tsare saboda zanga-zanga
- Ƙungiyar ta ce tsare yaran ya tauye musu haƙƙin da suke da shi na zuwa neman karatu a makaranta
- Tace za ta ɗauki matakin shari'a idan zuwa nan da sa'o'i 48 ba a saki yaran ba waɗanda ke cikin halin yunwa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Ƙungiyar ta jawo hankalin shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu kan yaran da aka tsare saboda zanga-zangar #EndBadGovernance.
Ƙungiyar SERAP ta buƙaci Shugaba Tinubu da ya yi amfani da ofishinsa wajen umartar ministan shari’a Mista Lateef Fagbemi, da ya ɗauki matakan gaggawa don tabbatar da sakin yaran guda 32 da sauran masu zanga-zanga.
SERAP ta bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa mai ɗauke da sa hannun mataimakin daraktanta, Kolawole Oluwadare da ta sanya a shafinta na yanar gizo.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
SERAP ta ba Tinubu wa'adin sa'o'i 48
SERAP ta ce yaran da sauran masu zanga-zangar ana tsare da su ne kawai don sun yi amfani da ƴancinsu na yin zanga-zanga cikin lumana
Ta buƙaci Tinubu ya umarci Fagbemi da hukumomin da suka dace da su tabbatar da ba da magunguna ga dukkan masu zanga-zangar ciki har da yara 32 da ke fama da yunwa saboda rashin lafiyarsu.
Ta bayyana cewa za ta ɗauki matakin shari'a idan nan da sa'o'i 48 ba a saki yaran ba daga tsarewar da aka yi musu.
"Tsare yaran 32 da ke fama da yunwa da rashin abinci mai gini jiki ya tauye haƙƙinsu na neman ilimi. Ya kamata yaran nan su kasance a makaranta, ba wai a tsare su ba."
"Za mu yi godiya idan an ɗauki shawarwarin da aka ba da nan da sa'o'i 48. Idan har zuwa lokacin ba mu ji ta bakinku ba, SERAP za ta yi la’akari da matakan da suka dace na doka don tilastawa gwamnatin ku bin wannan shawarar.
- Kolawole Oluwadare
Tinubu ya fara shirin janye ƙara kan yara
A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnatin tarayya ta fara shirin janye zarge-zargen da ake yi kan yaran da aka gabatar da su a gaban kotu.
Ministan Shari'a, Lateef Fagbemi shi ya fara daukar matakin kan yara 32 da aka gabatar a gaban Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja.
Asali: Legit.ng