Yan Bindiga Sun Mamaye Yanki a Arewa, Sun Kafa Jar Tuta Saboda Nuna Ƙarfin Iko

Yan Bindiga Sun Mamaye Yanki a Arewa, Sun Kafa Jar Tuta Saboda Nuna Ƙarfin Iko

  • Wasu yan bindiga sun mamaye wani yanki a jihar Taraba tare da kafa wata jar tuta bayan sun fatattaki al'ummar wuraren
  • Rahotanni sun tabbatar da cewa maharan sun mamaye wani tsauni a karamar hukumar Zing da ke iyakar jihohin Taraba da Adamawa
  • Hakan ya biyo bayan mamaye yankin a shekarar bara kafin hadin guiwar jami'an tsaro da yan banga su fatattake su a wancan lokaci

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Taraba - Rahotanni sun tabbatar da cewa yan bindiga sun mamaye wani yanki a jihar Taraba da ke Arewacin Najeriya.

An tabbatar da cewa yan bindiga sun kafa wata jar tuta a tsauni da ke karamar hukumar Zing a jihar Taraba.

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun sake kai mummunan hari, sun kashe uba da yaƴansa 2

Yan bindiga sun mamaye yanki a Taraba inda suka kafa jar tuta saboda ƙarfin iko
Wasu hatsabiban yan bindiga sun yi nasarar mamaye yankin Zing a jihar Taraba inda aka tabbatar sun kafa tuta. Hoto: Legit.
Asali: Original

Yan bindiga sun mamaye yanki a Taraba

Daily Trust ta ruwaito cewa maharan sun dawo makwanni kadan da suka wuce bayan mamayar yankin a karshen shekarar bara.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wani mazaunin yankin ya ce yan bindigar sun mamaye wurin da ke iyakar jihohin Taraba da Adamawa.

James Samuel ya tabbatar cewa an yi nasarar fatattakar yan bindigar da suka zauna a yankin shekarar da ta gabata da hadin guiwar jami'an tsaro.

An yi arangama da yan bindiga a bara

"Yan bindiga sun mamaye yankin a bara a daidai wannan lokaci da ake ɗebe amfanin gona, an yi nasarar fatattakarsu bayan shafe kwanaki ana arangama da hadin guiwar jami'an tsaro amma ga shi yanzu sun fara dawowa."
"Yanzu da nake magana, suna kan tsauni har sun kafa jar tuta amma mun sanar da yan banga a halin da ake ciki sun tunkare su."

Kara karanta wannan

Ana rigimar tsare yara 72, jami'an tsaro sun harbi daraktan fina finai a tumbi

James Samuel

Shugaban yan banga a jihar, Adamu Dantala ya tabbatar da labarin inda ya ce ya samu rahoton daga mazuna yankin.

Uba Sani ya koka kan ƙaruwar ta'addanci

Mun baku labarin cewa Gwamnan jihar Kaduna, Uba Sani ya nuna damuwa kan ƙaruwar sauya tunanin dalibai a manyan makarantu da ke Najeriya.

Uba Sani ya ce hakan bai rasa nasaba da rashin aikin yi da kuma talauci da daliban ke fama da shi inda ake saurin amfani da su.

Gwamnan ya ba da misalin dalibin da aka kama alburusai da dama a Jami'ar Tarayya da ke Dutsinma a jihar Katsina.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.