Jigon APC Ya Hango Dalilin da Zai Sa Yankin Arewa Kin Yin Adawa da Tinubu a 2027

Jigon APC Ya Hango Dalilin da Zai Sa Yankin Arewa Kin Yin Adawa da Tinubu a 2027

  • Jigon jam'iyyar APC a jihar Osun ya taɓo batun ƙudirin dokar gyaran haraji wanda ya jawo cece-kuce a cikin ƴan kwanakin nan
  • Oladele Oyelude ya ce yankin Arewacin Najeriya ba zai ƙi sake zaɓen Shugaba Bola Tinubu ba a 2027 saboda ƙudirin
  • Ya bayyana cewa masu son yin amfani da ƙudirin domin hana Tinubu ya samu ƙuri'u a yankin Arewa a 2027 ba za su yi nasara ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Osun - Darakta Janar na ƙungiyar Tinubu-Shettima Ambassadors, Oladele Oyelude, ya yi magana kan ƙudirin dokar gyaran haraji da ke gaban majalisa.

Jigon na APC ya ce masu shirin son yin amfani da ƙudirin dokar domin hana yankin Arewacin Najeriya zaɓar Tinubu a 2027, ba za su yi nasara ba.

Kara karanta wannan

Jam'iyyar APC ta gayawa gwamnatin Tinubu gaskiya kan tsadar rayuwa

Jigon APC ya magantu kan dokar gyaran haraji
Jigon APC ya ce yankin Arewa ba zai ki zaben Tinubu ba a 2027 Hoto: @DOlusegun
Asali: Twitter

Oladele Oyelude ya bayyana hakan ne yayin hira da manema labarai a birnin Osogbo babban birnin jihar Osun a ranar Asabar, cewar rahoton jaridar The Punch.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jigon APC ya ba da shawara

Jigon na APC a jihar Osun ya ce masu adawa da ƙudirin dokar kamata ya yi su sanya ƴan majalisunsu su ƙi amincewa da shi.

Ya bayyana cewa ƙudirin dokar gyara harajin zai kawo ci gaba a ƙasar nan ta hanyar sanya gwamnoni su zabura wajen nemo hanyoyin samun kuɗaɗen shiga.

Ya yi nuni da cewa majalisar tarayya za ta yi gyara kan inda ƙudirin yake da ƴan matsaloli.

"Na yi imanin cewa Arewa ba za ta yi adawa da sake zaɓen Tinubu ba saboda ƙudirin dokar gyaran haraji. Ɗan Arewa shi ne mataimakin shugaban ƙasa, don haka ba za su iya adawa da Tinubu ba saboda ƙudirin. Majalisar tarayya ce za ta yanke hukunci kan makomar kuɗirin.

Kara karanta wannan

Gwamnan APC ya ba da hutun kwanaki 2, ya bayyana dalili

"Idan har Arewa tana ganin ƙudirin bai cancanta ba, to ya kamata su nuna ƙin amincewarsu kan hakan ta hannun ƴan majalisar wakilai da sanatocinsu."

- Oladele Oyelude

APC ta ba gwamnatin Tinubu shawara

A wani labarin kuma, kun ji cewa jam’iyyar APC a jihar Bauchi, ta yi kira ga gwamnatin tarayya da ta ƙara himma wajen rage raɗaɗiin da ƴan Najeriya suke ciki.

Jam'iyyar APC ta kuma kira ga ƴan Najeriya da su riƙa yi wa shugabanninsu addu’o’in samun nasarar gudanar da ayyukansu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng