Gwamna Ya Kakaba Harajin N40,000 kan Mafi Ƙarancin Albashi? Fintiri Ya Yi Martani
- Gwamnatin jihar Adamawa ta ƙaryata labarin kakaba harajin N40,000 ga ma'aikatan jihar da ake yaɗawa
- Gwamna Ahmadu Umaru Fintiri da kansa ya mayar da martani kan jita-jitar inda ya ce maganar banza ce kawai
- Hakan ya biyo bayan zargin gwamnan ya sanya harajin N40,000 bayan fara biyan mafi ƙarancin albashin N70,000
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Adamawa - Gwamna Ahmadu Umaru Fintiri na jihar Adamawa ya yi magana kan zargin kakaba haraji ga ma'aikata.
Gwamna Fintiri ya musanta labarin da ake yaɗawa cewa ya saka harajin N40,000 ga ma'aikata bayan fara biyansu N70,000 a watan Agusta.
Harajin N40,000: Fintiri ya magantu kan rade-radin
Gwamnan ya bayyana haka ne a cikin wani faifan bidiyo da ya wallafa a shafinsa na X a yau Asabar 2 ga watan Nuwambar 2024.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamna Fintiri ya ce kamar yadda kowa ya sani ana cire haraji ga ma'aikata kuma wata biyu kenan ba a cire ba sai a watan Oktoba.
Ya koka kan yadda wasu wadanda ma ba su karbar albashi suke juya bayanin da cewa yana cire N40,000 daga cikin mafi ƙarancin albashi.
"Ba zan taba zama silar rugujewar wasu ba, kuma ba zan taba yiwa ma'aikata sata ba, abin da kullum ake yi ne bai kamata ya zamo dalilin bata wannan gwamnati ba."
"Wai muna biyan N70,000 amma mun karbi N40,000 ta yaya haka zai faru a gwamnatina? idan ban baku ba, ba zan kwata daga gare ku ba."
"Ta yaya zaka yi aiki ka ce ba zaka biya haraji ba, abu ne wanda kowa yasan ana karba, yaushe ya dawo wani labari da za a juya masa ma'ana."
- Ahmadu Umaru Fintiri
Fintiri ya ba yan Adamawa tabbacin inganta su
Fintiri ya ce yana mai tabbatarwa al'ummar Adamawa ba su ma fara ganin abubuwan alheri ba sai gaba.
Ya ce duk wanda ke neman ganin kuskurensu ya makara saboda kafin ya ankara zai tashi ya ga Adamawa ta zama Landan.
Legit Hausa ta yi magana da wani ma'aikataci a Gombe
Wani ma'aikaci a jihar Gombe da ya bayyana kansa a matsayin Isa kawai saboda tsaro ya soki tsarin gwamnonin bayan biyan albashin N70,000.
Isa ya ce a Gombe cuta ƙarara a kayi saboda lissafin karin kudin ba kowa ne ya fahimci yadda aka yi ba.
Ya koka da cewa wasu sun samu kudi a matakinsa amma shi kasa da duba 10 ya samu wanda ya rasa mene dalili.
Fintiri ya fara biyan mafi ƙarancin albashi
Kun ji cewa Gwamna Ahmadu Fintiri na jihar Adamawa ya zama na farko da ya fara biyan ma'aikata sabon mafi ƙarancin albashi na N70,000.
Ma'aikatan jihar Adamawa sun tabbatar da haka bayan karɓan albashin watan Agusta, sun kuma yabawa gwamnan.
Asali: Legit.ng