Yan Bindiga Sun Sake Kai Mummunan Hari, Sun Kashe Uba da Ƴaƴansa 2

Yan Bindiga Sun Sake Kai Mummunan Hari, Sun Kashe Uba da Ƴaƴansa 2

  • Wasu miyagu da ake kyautata zaton ƴan bindiga ne sun halaka manomi da ƴaƴansa biyu a yankin karamar hukumar Ivo a Ebonyi
  • Rahotanni sun bayyana cewa maharan sun kashe mutanen ne a gona yayin da suka tafi aiki kamar yadda suka saba
  • Ɗan majalisar tarayya mai wakiltar Ohaozara, Onicha da Ivo ya yi Allah waɗai da lamarin, ya buƙaci jami'an tsaro su ɗauki mataki

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Ebonyi - Ƴan bindiga sun kashe wani magidanci da ‘ya’yansa biyu a gona a garin Amaeze da ke yankin Ishiagu a karamar hukumar Ivo ta jihar Ebonyi.

Rahotanni sun nuna cewa an gano gawar mutanen uku da safiyar jiya Jumu'a bayan tsananta bincike saboda ba su koma gida ba.

Kara karanta wannan

A ƙarshe, hukumar INEC ta yi magana kan rikicin Majalisar dokokin jihar Ribas

Taswirar jihar Ebonyi.
Wasu miyagu da ake zargin ƴan bindiga ne suka kashe manomi da yaƴansa a Ebonyi Hoto: Legit.ng
Asali: Original

An gano gawar uba da ɗansa a gona

Wata majiya ta shaidawa jaridar Vanguard cewa ƴan uwa da dangi sun gano gawar manomin tare da ƴaƴansa da mugayen raunuka na sara da makami.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Da aka nemi jin ta bakinsa, jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, DSP Joshua Ukandu, ya ce har yanzu bai samu rahoton faruwar lamarin ba.

Sai dai shugaban karamar hukumar Ivo, Cif Emmanuel Ajah, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin, ya ce ya kara tsaurara matakan tsaro a yankin.

Ɗan majalisar wakilai ya yi Allah wadai

Haka kuma, dan majalisa mai wakiltar mazabar Ohaozara, Onicha da Ivo a majalisar wakilai ta ƙasa, Nkemkanma Kama, ya tabbatar da kisan mutanen uku.

"Na samu labarin kisan wasu manoma wanda wasu marasa kishin ƙasa, ƴan ta'adda, waɗanda ba su son zama lafiya suka aikata a garin Amaeze.

Kara karanta wannan

Gwamna Abba ya fadi matakin dauka kan gurfanar da yara a kotu

"Na yi Allah wadai da wannan aika-aika kuma ina kira ga hukumomin tsaro musamman sojoji da ƴan sanda su binciko duk masu hannu a lamarin domin doka ta yi aiki a kansu.
"A karshe ina kira ga al'umarmu kada ku ɗauki doka a hannu, ku bari jami'an tsaro su ɗauki matakin da ya dace."

Ƴan bindiga sun halaka ɗan kasuwa

A wani rahoton, kun ji cewa rundunar yan sanda a jihar Ebonyi ta tabbatar da kisan gilla da aka yi wa wani dan kasuwa mai shekaru 48, Micheal Nnaji.

Lamarin ya faru ne a ƙaramar hukumar Ohauku yayin da wasu yan bindiga suka kai masa hari da misalin karfe 9:45 na dare.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262