Katsina: Gwamna Ya Fadi Inda Ake Kyankyashe Yan Ta'adda cikin Sauki

Katsina: Gwamna Ya Fadi Inda Ake Kyankyashe Yan Ta'adda cikin Sauki

  • Gwamnan jihar Kaduna, Uba Sani ya nuna damuwa kan ƙaruwar sauya tunanin dalibai a manyan makarantu da ke Najeriya
  • Uba Sani ya ce hakan bai rasa nasaba da rashin aikin yi da kuma talauci da daliban ke fama da shi inda ake saurin amfani da su
  • Gwamnan ya ba da misalin dalibin da aka kama alburusai da dama a Jami'ar Tarayya da ke Dutsinma a jihar Katsina

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Katsina - Gwamna Uba Sani na jihar Kaduna ya koka kan yadda ake yaudarar dalibai a manyan makarantu.

Gwamna Uba Sani ya zargi cewa a manyan makarantu ne ake jirkita tunanin matasa wurin shiga ayyukan ta'addanci.

Kara karanta wannan

Gwamna Abba ya fadi matakin dauka kan gurfanar da yara a kotu

Gwamna ya tona asirin yadda ake samar da yan ta'adda a Arewa
Gwamna Uba Sani ya nuna damuwa kan yadda ake amfani da dalibai kan ayyukan ta'addanci. Hoto: Uba Sani.
Asali: Twitter

Uba Sani ya fadi silar ta'addanci

Gwamnan ya bayyana haka ne yayin bikin yaye daliban Jami'ar Gwamnatin Tarayya da ke Dutsinma a jihar Katsina, cewar Punch.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Uba Sani wanda kwamishinan ilimi a jihar Kaduna, Farfesa Muhammad Sani Bello ya wakilce shi ya ce talauci da rashin aikin yi su ne sila.

Ya ce abin takaici ne yadda ake amfani da dalibai a juya musu tunani saboda talauci da suke fama da shi.

Har ila yau, Uba Sani ya ba da misali yadda aka cafke dalibin Jami'ar da alburusai saboda ayyukan ta'addanci.

Yadda aka kama dalibi da alburusai a Katsina

"Abin da ya faru a FUDMA a kwanakin nan misali ne na abubuwan da ke faruwa."
"Yan sanda sun cafke dalibi da alburusai da dama domin ayyukan ta'addanci."

Kara karanta wannan

Pantami da mutane sun fusata da maka kananan yara a Kotu saboda zanga zanga

"Wannan ya nuna irin tasiri da kuma ƙaruwar jefa dalibai cikin ayyukan ta'addanci da wasu abubuwa da ba su dace ba."

- Uba Sani

Likita ta kubuta daga hannun yan bindiga

Kun ji cewa bayan shafe kusan watanni 10 a hannun ƴan bindiga, Dr. Ganiyat Popoola da ke aiki a asibitin ido na Kaduna ta shaƙi iskar ƴanci.

Shugaban kungiyar likitoci masu neman kwarewa watau NARD, Tope Zenith Osundara ya tabbatar da sako likitar.

Ranar 27 ga watan Disambar 2023 aka yi garkuwa da likitar tare da mijinta da wani ɗan uwanta da ke zaune tare da su a Kaduna.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.