Hukumar Gidajen Yari Ta Yi Magana kan Zargin Tsare Yara 72, Ta Fayyace Gaskiya
- Hukumar gidajen yari a Najeriya ta yi martani kan jita-jitar cewa ita ta tsare yara 72 da aka gurfanar da su a gaban kotu
- Hukumar ta ce duk labarin da ake yaɗawa cewa ta tsare su a gidan kaso ba gaskiya ba ne saboda doka ba ta ba da damar haka ba
- Hakan ya biyo bayan zargin ajiye yaran na tsawon watanni a gidan kaso inda wasu ke ganin sun yi kankanta duba da shekarunsu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
FCT, Abuja - Hukumar kula da gidajen gyaran hali a Najeriya ta yi magana kan tsare kananan yara 72.
Hukumar ta ƙaryata labarin da ake yaɗawa cewa ta tsare yaran a gidan yarin Kuje da ke birnin Tarayya Abuja.
Zanga-zanga: A karshe, hukumar gidajen yari ta magantu
Mai magana da yawun hukumar, Abubakar Umar shi ya tabbatar da haka a yau Asabar 2 ga watan Nuwambar 2024, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Umar ya ce a tsarin dokar hukumar jami'ansu ba su da hurumin tsare kananan yara a wurin da aka tanadar saboda manya.
Ya kuma ce a dokar, an ba su damar kin karbar karin wasu mutane domin tsarewa idan har ya tabbata inda za a ajiye su ya cika babu masaka tsinke.
Hukumar ta ki amincewa da tsare yara 72
"Ana ta yada rade-radi kan yaran da aka gurfanar da su a gaban Babbar Kotun Tarayya a Abuja, an ce kafin gurfanar da yaran da ake zargi da cin amanar kasa an tsare su gidan yari na manya da ke Abuja."
"Babu kamshin gaskiya a ciki kuma a doka babu inda za a ajiye yara ƙanana wurin da aka ware domin tsare manya."
"Muna mai tabbatar muku da cewa mun ki amincewa da ajiye yaran a wurin tsare manya ba kamar yadda ake yaɗawa ba."
- Abubakar Umar
Hukumar ta ba al'umma tabbacin za ta cigaba da aiki cikin kwarewa da kare hakkin dan Adam daidai da dokar Majalisar Dinkin Duniya kan laifuffukan yara ƙanana.
Sanata ta yi Allah wadai ta tsare yara
Kun ji cewa Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan da ke wakiltar Kogi ta Tsakiya ta yi Allah wadai da tsare ƙananan yara ba bisa ka'ida ba.
Sanata Natasha ta ce akwai tsantsar rashin tausayi da adalci a tsare yara ƙanana ba tare da kulawa ta abinci ba.
Asali: Legit.ng