Dubu Ta Cika: An Kama Kasurgumin Ɗan Bindiga da Ya Addabi Mutane a Sakkwato
- Dakarun sojojin Najeriya sun yi nasarar cafke jagoran ƴan bindiga, Abubakar Ibrahim wanda ake kira da Habu Dogo a jihar Sakkwato
- Rundunar sojoji ta ce Habu Dogo na cikin shugabannin ƴan ta'adda da hukumomin tsaro ke nema ruwa a jallo a Najeriya da Nijar
- Mai magana da yawun hedkwatar tsaro ta kasa, Manjo Janar Edward Buba ne ya bayyana hakan a wata sanarwa ranar Asabar, 2 ga watan Nuwamba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja - Rundunar sojin Najeriya ta ce dakarunta a yankin Arewa maso Yamma sun kama wani shugaban 'yan ta'adda da ake kira Abubakar Ibrahim.
Abubakar Ibrahim wanda aka fi sani da Habu Dogo ya shiga hannun dakarun sojoji ne a makon da ya wuce a jihar Sakkwato.
Daraktan yaɗa labarai na hedkwatar tsaro (DHQ), Manjo Janar Esward Buba ne ya bayyana hakan a wata sanarwa ranar Asabar, 2 ga Nuwamba, Channels tv ta ruwaito.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sojoji sun kama Habu Dogo a Sakkwato
Ya ce sojojin sun samu wannan nasara ne a kokarinsu da suke na wanzar da zaman lafiya tare da kakkaɓe duk wani nau'in ta'addanci a ƙasar nan.
Habu Dogo dai kasurgumin ɗan ta'adɗa ne da hukumomin tsaro a Najeriya ɗa Jamhuriyar Nijar ke nema ruwa a jallo saboda yadda ya addabi jama'a a ƙasashen.
Kakakin DHQ, Edward Buba ya bayyana cewa sojoji sun yi nasarar cafke Habu Dogo a kauyen Rumji da ke ƙaramar hukumar Illela a jihar Sakkwato.
An kama kwamandojojin IPOB a Anambra
Hakazalika, dakarun sojoji a yankin Kudu maso Gabas sun kama kwamandojin kungiyar 'yan ta'adda IPOB/ESN guda 7.
A cewar sanarwar, ‘yan ta’addan IPOB/ ESN da aka kama sun hada da; Dr Nnamdi Chukwudoze and Chigozie Ezetoha (AKA Chapet) a ƙaramar hukumar Ihila a Anambra.
Muƙaddashin hafsan sojin kasa ya kama aiki
A wani rahoton, an ji cewa muƙaddashin shugaban rundunar sojojin kasa ta Najeriya da Bola Tinubu ya naɗa ya kama aiki a ofishinsa da ke Abuja ranar Jumu'a
Manjo Janar Olufemi Oluyede zai riƙe kujerar COAS gabanin dawowar Laftanar Janar Taoreed Lagbaja wanda ya tafi hutun rashin lafiya.
Asali: Legit.ng