Yajin Aiki: Gwamnatin Tinubu Ta Saki Kuɗi, An Fara Biyan Albashin NASU

Yajin Aiki: Gwamnatin Tinubu Ta Saki Kuɗi, An Fara Biyan Albashin NASU

  • Gwamnatin tarayya ta tabbatar da fara biyan albashin da ma'aikatan jami'o'i suke bi bashi wanda ya sa suka tsunduma yajin aiki
  • Ofishin Akanta Janar ta kasa ne ya bayyana hakan a wata sanarwa mai ɗauke da sa hannun Bawa Mokwa ranar Asabar, 2 ga watan Nuwamba
  • Tun farko dai kungiyoyin ma'aikatan jami'o'i SSANU da NASU sun shiga yajin aikin sai baba ta gani a makon da ya wuce kan rashin biyansu albashi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - Gwamnatin tarayya ta fara biyan ma'aikatan jami'o'i da waɗanda suka yi ritaya hakkokinsu da suka biyo bashi.

Daraktan yaɗa labarai na ofishin akanta janar ta ƙasa, Bawa Mokwa ya tabbatar da haka a wata sanarwa da ya fitar ranar Asabar.

Kara karanta wannan

Ana rigimar tsare yara 72, jami'an tsaro sun harbi daraktan fina finai a tumbi

Bola Tinubu
Gwamnatin tarayya ta fara biyan ma'aikatan jami'o'i abashin da suke bi bashi Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Ya ce tuni aka fara biyan ƴaƴan kungiyar ma'aikatan jami'o'i watau NASU kuma da yawansu sun tabbatar da kudi sun shiga asusunsu, Punch ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamnatin Tinubu ta fara biyan albashin NASU

Sanarwar ta ce:

"Gwamnatin tarayya ta saki kudi domin biyan albashin ma’aikatan jami'o'in tarayya. Haka nan kuma an fitar da kudade domin biyan hakkokin ‘yan fansho a karkashin kungiyar ‘yan fansho ta Najeriya."

Ofiahin Akanta Janar (OAGF) ya sake jaddada kudirin gwamnatin tarayya na kula da jin dadi da walwalar ma’aikatan Najeriya da wadanda suka yi ritaya.

Yadda NASU ta shiga yajin aiki

A ranar Litinin da ta wuce kwamitin hadin gwiwa na SSANU da NASU ya ayyana shiga yajin aikin sai baba-ta-gani kan rashin biyansu albashi na watanni hudu.

Tun daga wannan lokacin harkokin tafiyar jami'o'i suka tsaya cik, wanda hakan ya zama cikas ga karatun ɗalibai.

Kara karanta wannan

Dubu ta cika: An kama ƙasurgumin ɗan bindiga da ya addabi mutane a Sakkwato

A wata hira ranar Laraba, shugaban kungiyar manyan ma'aikatan jami'o'i watau SSANU, Mohammed Ibrahim, ya ce wata huɗu kenan ba su ga albashinsu ba.

Ya ce hatta shugabannin jami'o'i (VCs), da sauran jagorori ba a biya su albashi ba shiyasa suka shiga yajin aiki kuma ba za su janye ba har sai an biya su haƙkinsu.

A yanzu dai gwamnati ta ce an fara biyan albashin waɗannan watanni da aka rikewa ma'aikatan domin rarrashinsu su koma aiki, kamar yadda The Nation ta kawo.

ASUU ta yi barazanar shiga yajin aiki

A wani rahoton, kun ji cewa ƙungiyar ASUU ta jaddada barazanar tafiya yajin aiki matukar gwamnati ta ki amincewa da biya mata bukatunta.

Shugaban kungiyar reshen jami'ar Nsukka, Raphael Amokaha ya jaddada matsayarsu yayin da gwamnati ke jan kafa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262