Shugaban 'Yan Sanda Ya Fadi Shirin da Aka Yi da Ya Sa Yara Suka Suma a Kotu

Shugaban 'Yan Sanda Ya Fadi Shirin da Aka Yi da Ya Sa Yara Suka Suma a Kotu

  • Sufeto-Janar na ƴan sandan Najeriya, Kayode Egbetokun, ya yi tsokaci kan sumar da wasu daga cikin yaran da aka gurfanar a gaban kotu suka yi
  • Shugaban ƴan sandan ta hannun kakakin rundunar ya bayyana cewa sumar da yaran suka yi shiri ne kawai domin jawo hankalin mutane
  • Kakakin ƴan sandan ya sanar da cewa bayan faurwar lamarin an ba yaran kulawar da ta dace

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Sufeto-Janar na ƴan sanda, Kayode Egbetokun, ya yi magana kan sumar da wasu daga cikin yaran da gurfanar a gaban kotu suka yi.

Shugaban ƴan sandan ya bayyana cewa sumar da shida daga cikin yaran suka yi, kafin a gurfanar da su a gaban kuliya, wani shiri ne da aka shirya domin jawo hankulan mutane.

Kara karanta wannan

Gwamna Abba ya fadi matakin dauka kan gurfanar da yara a kotu

Yaran da aka tsare a kotu
Kayode Egbetokun ya ce sumar yara a kotu shiri ne Hoto: @PoliceNG, @YeleSowore
Asali: Twitter

Shugaban ya yi magana kan sumar yara

Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da kakakin rundunar ƴan sandan Najeriya, Olumuyiwa Adejobi ya fitar a madadin shugaban ƴan sandan a shafin X.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shugaban ƴan sandan ya jaddada cewa, ba tare da ɓata lokaci ba, an ba su tallafin da ya dace.

"Wani lamari da ba a yi tsammani ba a kotu ya sa shida daga cikin waɗanda ake zargi sun suma, wanda hakan ya sanya suka jawo hankalin manema labarai a wani yanayi wanda aka shirya domin jawo surutu."
"An gaggauta ba da tallafin magunguna ga waɗannan mutanen, wanda hakan ya nuna jajircewar ƴan sanda na kula da jindaɗin mutanen da ke tsare a hannunta ba tare da la'akari da zarge-zargen da suke fuskanta."

- Olumuyiwa Adejobi

Ƙwankwaso ya soki kai yara kotu

Kara karanta wannan

Kwankwaso ya soki gurfanar da kananan yara kotu, ya ba gwamnati shawara

A wani labarin kuma, kun ji cewa tohon gwamnan jihar Kano, Rabi'u Kwankwaso, ya yi Allah-wadai da gurfanar da ƙananan yara da rundunar ƴan sanda ta yi a Abuja bisa zarginsu da gudanar da zanga-zanga.

Da yake bayyana kaɗuwarsa da faruwar lamarin, Kwankwaso ya nuna matuƙar damuwarsa kan abinda aka yi wa yaran na wahalar da su a yayin da suke tsare tare da kawo su gaban kotu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng