Yadda Farashin Man Feturin Ɗangote Ya Fi na Wasu Wurare Tsada, IPMAN Ta Yi Bayani

Yadda Farashin Man Feturin Ɗangote Ya Fi na Wasu Wurare Tsada, IPMAN Ta Yi Bayani

  • Kungiyar daillalan man fetur masu zaman kansu IPMAN ta bayyana cewa man feturin Ɗangote ya fi na sauran wurare tsada
  • Mataimakin sakataren IPMAN na ƙasa, Yakubu Suleiman ya ce burin ƴan kasuwa su ɗauko kaya da arha ta yadda za su saukaƙawa mutane
  • Ya ce ba zai yiwu dillalai na ganin wurin da za su samu fetur a farashi mai sauƙi ba kuma su tafi matatar Ɗangote su saya da tsada

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Kungiyar dillalan mai masu zaman kansu IPMAN ta bayyana cewa farashin man feturin matatar Ɗangote ya fi tsada fiye da sauran wuraren da ake sayo mai.

IPMAN ta ce wannan ya sa ƴaƴanta suke gujewa sayen man feturin Ɗangote, su saya daga wasu manyan wuraren kasuwancin fetur a faɗin ƙasar nan.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun hallaka mutane masu yawa a mahaifar tsohon gwamna

Matatar Ɗangote.
IPMAN ta bayyana dalilin kauracewa sayen mai a matatar Ɗangote Hoto: Contributor
Asali: Getty Images

Mataimakin sakataren IPMAN na ƙasa, Yakubu Suleiman ne ya faɗi haka da yake jawabi a cikin shirin safe na gidan talabijin na Arise ranar Juma'a.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda man feturin Ɗangote ya fi tsada

Yakubu ya ce yan kasuwa sun gwammace su sayi fetur a wuri mai arha maimakon matatar Ɗangote, jaridar The Cable ta rahoto.

"Alal misali, idan matatar Ɗangote na sayar lita kan N1,000, wani wurin kuma suna sayarwa a farashin N900, ba zai yiwu dan muna da wata alaƙa da Ɗangote mu tilastawa mambobinmu su saya da tsada ba.
"Za mu tafi mu sayo fetur a wurin da ya fi arha, inda za mu samu riba. A iya sanina a makon jiya, farashin man feturin Ɗangote ya fi tsada.
"Farashin danyen mai yana sauka a duniya, amma farashin Dangote ya kai Naira 995 a kowace lita, sannan kai zaka yi jigilar kayanka, idan kuka duba tsdaar sufuri, nawa kuke tunanin zamu sayar ga mutane?"

Kara karanta wannan

'Yan kasuwa sun bi sahun NNPCL, sun ƙara farashin litar man fetur a Najeriya

- Yakubu Suleiman.

IPMAN na kokarin saukakawa jama'a

Ya ƙara da cewa kungiyar IPMAN na kokarin taimakawa kasar nan, musamman a wannan mawuyacin lokaci da mutane ke cikin wahala da kuncin rayuwa.

Yakubu ya ce dillalan mai na fatan sayo kaya a farashi mai rahusa ta yadda za su sayarwa mutane a farashi mai sauƙi.

Yan kasuwa sun tashi farashin fetur

A wani rahoton na daban, an ji cewa yan kasuwa sun ƙara farashin man fetur kwanaki kaɗan bayan gidajen man NNPCL sun yi ƙari a Najeriya.

Farashin litar mai a gidajen man ƴan kasuwa masu zaman kansu ya tashi daga N1,060 zuwa tsakanin N1,100 da N1,200.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262