'Yan Ta'adda Sun Hallaka 'Yan Banga a Wani Kazamin Hari

'Yan Ta'adda Sun Hallaka 'Yan Banga a Wani Kazamin Hari

  • Ana tsoron cewa wasu miyagun ƴan ta'adda sun kai farmaki a jihar Neja inda suka hallaka jami'an tsaro na ƴan banga
  • Ƴan ta'addan sun hallaka ƴan bangan ne a ƙaramar hukumar Mariga a harin da suka kai ranar Alhamis, 31 ga watan Oktoban 2024
  • Shugaban majalisar dokokin Neja ya buƙaci rundunar sojoji ta daina ƙaryata batun cewa akwai ƴan ta'adda a sansaninta na Kontagora

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Neja - Wasu ƴan ta’adda sun kashe ƴan banga 13 a ƙaramar hukumar Mariga da ke jihar Neja.

Ƴan ta'addan sun hallaka ƴan bangan ne a lokacin da suka yi ƙoƙarin kai hari cikin wani ƙauye da safiyar Alhamis.

'Yan ta'adda sun hallaka 'yan banga a Neja
'Yan ta'adda sun kai.hari a jihar Neja Hoto: Legit.ng
Asali: Original

Ƴan ta'adda sun kai hari a jihar Neja

Kara karanta wannan

An yi barnar rayuka bayan 'yan banga sun fafata da 'yan bindiga

Jaridar The Nation ta rahoto cewa ƴan ta’addan sun kuma yi awon gaba da matafiya a cikin motoci biyar a lokacin da suka tare hanyar Minna zuwa Kontagora a yammacin ranar Alhamis.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hakazalika a yammacin ranar Laraba an sace wani jami’in soja a gonarsa yayin da aka sace wasu manoma tara tare da kashe uku daga cikinsu.

Kakakin majalisa ya ba sojoji shawara

Kakakin majalisar dokokin Nijar, Abdulmalik Sarkindaji, ya nemi rundunar sojoji cewa ta daina ƙaryata kasancewar ƴan bindiga a sansanin horonta da ke Kontagora. 

Ya ce shaidun da ake da su sun nuna cewa ƴan bindigan sun mamaye wasu sassan sansanin horar da sojojin.

"Mutanen ƙauyukan sun ce sansanin sojojin ya koma mafakar ƴan bindiga waɗanda ke fitowa daga cikin dajin suna kai musu hari, su sace mutane sannan su tafi da su zuwa cikin dajin.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun hallaka mutane masu yawa a mahaifar tsohon gwamna

"Hatta mutanen da aka sako bayan an biya kuɗin fansa sun ce an kai su dajin ne kuma suna hango sansanin sojojin na Kontagora daga inda ƴan bindigan suka ajiye su."

- Abdulmalik Sarkindaji

Ƴan banga sun fafata da ƴan ta'adda

A wani labarin kuma, kun ji cewa ƴan banga sun yi musayar wuta da ƴan bindiga a jihar Plateau da ke yankin Arewa ta Tsakiya.

Aƙalla mutane huɗu ne suka rasu a arangamar da aka yi tsakanin ƴan bindiga da ƴan banga a ƙauyen Dogon Ruwa da ke gundumar Bashar a karamar hukumar Wase ta jihar.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng