COAS: Muƙaddashin Hafsan Sojojin Ƙasa da Tinubu Ya Naɗa Ya Kama Aiki a Abuja
- Muƙaddashin shugaban rundunar sojojin kasa ta Najeriya da Bola Tinubu ya naɗa ya kama aiki a ofishinsa da ke Abuja ranar Jumu'a
- Manjo Janar Olufemi Oluyede zai riƙe kujerar COAS gabanin dawowar Laftanar Janar Taoreed Lagbaja wanda ya tafi hutun rashin lafiya
- Babban hafsan hafsoshin tsaro CDS, Christopher Musa ya miƙa tutar sojoji ga muƙaddashin hafsun sojojin kasar a hedkwatar tsaro
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
FCT Abuja - Muƙaddashin hafsan rundunar sojojin ƙasa ta Najeriya (COAS), Manjo Janar Olufemi Oluyede ya kama aiki a ofishinsa da ke hedkwatar sojoji a Abuja.
Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya naɗa Oluyede ya riƙe mukamin gabanin dawowar hafsan sojojin, Laftanar Janar Taoreed Lagbaja, wanda ya ɗauki hutun rashin lafiya.
A wurin taron mika masa ragama a hedkwatar tsaro yau Jumu'a, sabon muƙƙadashin COAS ya godewa Bola Tinubu bisa ganin ya cancanta kuma ya naɗa shi.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya kuma yi addu’ar Allah ya ba wa hafsan rundunar sojijin, Laftanar Janar Taoreed Lagbaja lafiya.
Naɗin muƙaddashin COAS bai saɓawa doka ba
Hakan dai na kunshe ne a wata sanarwa da rundunar sojojin ƙaa ta wallafa a shafin X mai ɗauke da hannun kakakinta, Onyema Nwachukwu.
Babban hafsan hafsoshin tsaro, Janar Christopher Musa, ya jaddada cewa nadin Oluyede ya yi daidai da dokar sojoji ta 2004.
Babban abin da ya fi daukar hankali a wurin taron shi ne lokacin da CDS Musa ya mika tutar rundunar soji a hukumance ga sabon mukaddashin hafsan sojin kasa.
Sabon hafsan sojin ya nemi goyon baya
Mukaddashin COAS ya kuma nemi goyon bayan dukkan jami’an soji da ‘yan Najeriya wajen tunkarar kalubalen tsaro da ke addabar kasar nan.
Oluyede ya yi alkawarin biyayya ga babban kwamandan sojojin kasa da kuma kundin tsarin mulkin tarayyar Najeriya.
Hedkwatar tsaro ta musanta kwace sansanin soji
A wani labarin, an ji cewa hedkwatar tsaron Najeriya ta musanta zargin cewa yan bindiga sun kwace sansanin sojoji a Kontagora a jihar Neja.
Mai magana da yawun DHQ, Manjo Janar Edward Buba ya ce ko inci ɗaya ƴan ta'adda ba su kwace daga hannun sojoji ba.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng