Kotu Ta Sake Takaita Tsohon Gwamnan CBN, Ta Kwace Dala Miliyan 2.04 da Kadarori
- A karshe babbar kotun tarayya mai zama a Legas ta kwace wasu kuɗaɗe da kadarori da ake zargin suna da alaƙa da Emefiele
- Kotun ta kwace su saboda babu wanda ya zo da hujjar cewa na shi ne tun da ta bada umarnin karbe su na wucin gadi
- Tsohon gwamnan CBN, Godwin Emefiele na ci gaba da fuskantar shari'a kan tuhume-tuhumen cin hanci da halatta kudin haram
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Lagos - Babbar kotun tarayya mai zama a Legas a ranar Juma’a ta bayar da umarnin kwace makudan kudade har Dala miliyan 2.045 da ke da alaƙa da Godwin Emefiele.
Kotun ta kuma karɓe wasu manyan kadarori bakwai da takaddun hannun jari masu alaka da tsohon gwamnan babban bankin Najeriya, Godwin Emefiele.
Channels tv ta ce Mai shari’a Deinde Dipeolu shi ne ya ba da umarnin a kwace kudaden da kuma takaddun hannun jari biyu na Queensdorf Global Fund Limited Trust.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kotu ta kwace kudi masu alaƙa da Emefiele
Wannan dai na nufin an karɓe waɗannan makudan kudi da kadarorin har abada saboda babu wanda ya zo ya ce na shi ne bayan kwacewar farko ta wucin gadi.
Kotun ta kara da cewa ta kwace manyan kadarori bakwai saboda zargin da kudin sata tsohon gwamnan CBN ya mallake su, ba halatattun kudi ba ne.
Kazalika Kotun ta ce Emefiele ya kasa bayar da takardu ko hujjojin da za su nuna cewa ya mallaki kadarorin ta halattaciyar hanya.
Tsohon gwamnan CBN ya musanta alaƙa da kamfanoni
Tun farko dai Emefiele ya musanta wata alaka da kamfanonin da aka sayi kadarorin da sunayensu, sannan kuma kamfanonin ba su zo kotu sun yi bayani ba.
Hukumar EFCC ta bayyana sunayen kamfanonin da suka haɗa da Amrash Ventures Limited, Modern Hotels Limited da Finebury Properties Limited.
Sauran sun kunshi Fidelity Express Services Limited, H & Y Business Global Limited da kuma SDEM Erectors Nigeria Limited.
EFCC ta saƙe bankado badaƙalar Emefiele
A wani labarin, kun ji cewa tsohon gwamnan CBN, Godwin Emefiele ya sake shiga wata sabuwar matsala yayin da aka bankado wata badakar N18bn a 2014.
Wani bincike da aka ce hukumar EFCC ta gudanar ya nuna cewa Emefiele ya yi amfani da N18bn wajen buga N1bn da sayen kayan sitamfi.
Asali: Legit.ng